Martani ga kalaman Gwamna Sule Lamido

Shi kuwa Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi (08095968366), ya aiko da tsokaci a matsayin martani ga kalaman da Gwamna Sule Lamido ya yi game da jam’iyyar adawa ta APC:Abin Dariya, wai yaro ya tsinci Hakori. Na yi mamakin Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, da ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta APC ba za ta […]

Martani ga kalaman Gwamna Sule Lamido
Martani ga kalaman Gwamna Sule Lamido

Shi kuwa Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi (08095968366), ya aiko da tsokaci a matsayin martani ga kalaman da Gwamna Sule Lamido ya yi game da jam’iyyar adawa ta APC:
Abin Dariya, wai yaro ya tsinci Hakori. Na yi mamakin Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, da ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta APC ba za ta iya mulkar Najeriya ba. Saboda yadda aka samar da jam’iyyar ta APC ya saba da jam’iyyu masu tsantsar akidar dimokuradiyya. Ya kara da cewa jam’iyyar an samar da ita ne don bukatun wasu daidaikun mutane.
Lallai ta kara tabbata cewa, laifi tudu ne. Da yawa mutane take nasu suke su hango na wani. In ban da haka, ta yaya dan Jam’iyyar PDP mai mulki, zai zargi jam’iyyar adawa a kan abin da shi ya fi dacewa a zarga?
To amma abin tambaya ga Sule Lamido shi ne, shin a wannan hali da Najeriya take ciki, wace jam’iyya ce wadda za ta iya kubutar da rayuka da dimbin dukiyoyin da ake kashewa kusan kullum sakamakon rashin tsaro? Shin jam’iyyar PDP da ta shekara sama da 10 tana mulki, ta iya wadata al’umma da tsaron rayukansu, dukiyoyinsu, mutuncinsu da addininsu? Me Sule zai ce kan matsalar fatara, cin hanci, yawaitar fashi da makami, rashin aiki ga matasa, fyade da shaye-shaye da ke faruwa a kullum a kasar nan?
Duk da ba ni ne Sule Lamido ba, amma na san zai iya ba da amsar cewa PDP ba ita ce jam’iyyar da za ta iya maganin wadannan matsalolin da suka dabaibaye Najeriya ba. Don ta gaza samar da ababen more rayuwa ga ’yan kasa, wadanda ta tarar lokacin da ta hau mulki su ma sun salwanta, irin su, Nitel, Nigeria Airline, jiragen kasa, kamfanonin tace man fetur, P.T.F, kamfanin samar da wutar lantarki NEPA da kuma cire tallafin man fetur (wanda ’yan kasa ke samun saukin sayen mai) sannan ga tashin hankali da rashin zaman lafiya ga ’yan kasa.
Na san Lamido ba zai yi kasa a gwiwa ba wajan amsa cewar PDP ta gaza wajan samar wa matasa aikin yi. Dubi dai yadda aka rasa rayuka na mutane 20, sakamakon jarabawar daukar ma’aikatan Hukumar-Shige-Da-Ciki, inda mutane kusan miliyan ne suka je neman aikin. Ballantana a je ga samar da likitoci kwararru a asibitoci, ingantaccen ilimi, tsaftataccen ruwan sha, wutar lantarki, ingantattun hanyoyi da raya karkara, duk sun zama labari.
Dubi dai irin wadannan abubuwan, dole al’ummar Najeriya su yi kokarin canza jam’iyya don gazawar jam’iyyar da ke jagorancin kasar nan.
Daga karshe, ina kira ga Sule Lamido da ya gyara gidansa kafin ya hango gidan wani. Duk da an ce laifi tudu ne, to shi dai ya take na jam’iyyarsa yana kokarin hango na jam’iyyar adawa.