Martani: Gwamnatin APC Da Zaben Shugaban Majalisar Katsina

Hankalina ya dauku ga wani rubutu ko in ce soki-burutsu da wani dan jarida, danjuma Katsina ya rubuta kuma aka buga a shafin ‘Ra’ayi’ (shafi na 11) na jaridar Aminiya ta ranar Juma’a 19 ga watan Yuni, 2015. Na kira rubutun ko ra’ayin da soki-burutsu saboda ganin yadda marubucin ya yi ta kwan-gaba kwan baya […]

Martani: Gwamnatin APC Da Zaben Shugaban Majalisar Katsina
Martani: Gwamnatin APC Da Zaben Shugaban Majalisar Katsina

Hankalina ya dauku ga wani rubutu ko in ce soki-burutsu da wani dan jarida, danjuma Katsina ya rubuta kuma aka buga a shafin ‘Ra’ayi’ (shafi na 11) na jaridar Aminiya ta ranar Juma’a 19 ga watan Yuni, 2015.

Na kira rubutun ko ra’ayin da soki-burutsu saboda ganin yadda marubucin ya yi ta kwan-gaba kwan baya tare da tufka da warwara wajen bayyana shriritarsa, inda ya yi ta shaci-fadi domin ganin ya shafa wa Jam’iyyar APC da Gwamnan Adalci, Dallatun Katsina, Aminu Bello Masari kashin kaji.
Marubucin ya yi ikirarin wai APC a Katsina ta fara saka da mugun zare, inda wai a cewarsa ta karya alkawura har guda uku cikin wadanda ta yi a lokacin da take yakin neman zabe. Ni kuwa n ace wannan rubutu ba komai yake nufi ba sai neman suna da son a sani.
Na farko dai mai rubutun ya zargi mai girma Gwamna da karya alkawari, kawai don ya tare a sabon gidan gwamnatin da gwamnatin da ta shude ta gina. Ni kuwa na ce a ina ne Dallatu ya yi alkawarin cewa ba zai zauna sabon gidan gwamnati ba? A wace kafa ya yi wa al’ummar Jihar Katsina wannan batu?
A cewar mai zargin, wanda ya nufi bata wa sabuwar gwamnati mai niyyar adalci suna, ya ce wai a yayin yakin neman zabe, ya ji Sabo Musa Hassan wai ya yi magana a gidan rediyon bision FM Katsina, inda ya ce wai idan APC ta kafa gwamnati, ba za ta shiga sabon gidan gwamnati ba, wai asibiti za ta mayar da shi. Ya ce wai shi Malam Sabo jigo ne a APC kuma wanda ya yi yaki don dora sabuwar gwamnatn bisa mulki.
Ni kuwa na ce wannan shi ne abin dariya, wai yara sun tsinci hakori. Abin tambaya a nan shi ne, idan ana maganar jigogin jam’iyyar APC a Jihar Katsina, wane ne Sabo Musa kuma mene ne mukaminsa da har zai iya bugun gaba ya dauki alkawari a madadin dan takarar gwamna sukutum? A lokacin da ake yakin neman zabe, Gwamna Masari bai da jami’in hulda da kafafen watsa labarai? Yaushe Sabo Musa ya zama kakakin Masari da zai ari bakinsa ya ci masa albasa? Kada ka manta, Sabo Musa dan PDP kuma dan gani-kashe-nin tsohon Gwamna Shema. Bai tashi dawowa APC ba har sai da aka zo gab da zabe. Don haka a yaushe ne har ya samu gindin zama ya ari bakin Gwamna Masari ya yanke masa wannan hukunci na cewa ba zai zauna gidan gwamnati ba?
Babu inda marubucin ra’ayin nan ya ba ni dariya da kunya ma sai inda ya ce: “Na san na daukar ma kaina duk ranar da na ga Gwamnan Katsina, koda kuwa a wajen jana’iza ne, sai na tambaye shi, me ya sa yake zaune a cikin sabon gidan gwamnati; duk da ikirarin APC cewa ba za su zauna a ciki ba?”
Wadannan kalamai sun nuna irin bakin halin mai furta su. Wai zai tuhumi gwamna koda a wajen jana’iza ne! Allah kiyashe mu da wannan bakar adawa. Kuma ga shi wai ya kira kansa dan jarida! Ai da ya kamata ya ce shi dan siyasa ne, da sai a fi gane kaifiyyar gabarsa da sabon Gwamnan da Allah Ya nada wa Katsinawa. Idan ba shirme da makauniyar adawa ba, ta yaya za ka tuhumi mutum da laifin da bai aikata ba? Domin dai ko za a daure shi ta baya, marubucin nan ba zai iya kawo shaida sahihiya, inda Masari ya dauki wannan alkawari ba.
Abu na gaba da mai ra’ayin nan ya bijiro da shi, shi ne zargin wai sabuwar gwamnati ta yi katsalandan da babakere wajen zaben Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, inda aka zabi matashi, Alhaji Aliyu Maduru. Ya ce wai Masari ya karya alkawarin da ya yi na bin doka da oda wajen tafiyar da gwamnatinsa. Ba kunya ba tsoro kuma marubucin ya yi wa Shugaban kasa Buhari kage, ya ce wai zaben nan da aka yi a Majalisar Katsina wai ya bata masa rai. Ni kuwa na ce Shugaban kasar da bai sanya baki a zaben Majalisun kasa ba sukutum, saboda me zai sauko kasa har ya nuna wata bukata a karamar majalisa ta jiha? Lallai wannan marubucin bai ma san wane ne Buhari ba kuma bai san me ake kira majalisa da aikinta ba.
Marubucin, a yayin warware zarginsa, ya ce wai kafin zaben Shugaban Majalisar, sai da aka canja wani kuduri da ya saba wa sunnar majalisar ta baya. Abin tambaya ga mai ra’ayin nan shi ne, Wa ya canja kudurin dokar tafiyar da majalisar? Wane kuduri ne, me kudurin ya ce? Idan ’yan majalisa aikinsu ne kafa doka, sun yi laifi ne idan sun kafa ko sun canja wata doka? Kuma ka ce tsoffin ’yan majalisa ne suka canja kudurin, kwana uku kafin su fita. Kada ka mance mafi yawansu ’yan PDP ne ba APC ba. Ka ce wai wani ya ba su Naira dubu 500 kowannensu domin canza waccan doka. To wane ne ya ba su wadannan kudi da ka yi zargi, tsohuwar gwamnati ko kuwa gwamnatin da ba ta ma kai ga shigowa ba a lokacin da aka canja dokar?
Mai rubutun ya yi ikirarin wai ba a bi ka’ida ba wajen zaben Shugaban Majalisar, to ta yaya? Ya kamata ka zayyano mana ka’idojin da aka karya idan ka san su, balle ma ba ka san komai ba sai shaci-fadi kawai.
Idan marubucin bai san tarihi ba, ya je ya bincika tarihi Majalisar Jihar Katsina tun daga 1999 da aka dawo mulkin Dimokuradiyya, ba a taba yin zaben Shugaban Majalisa sahihi kamar wannan karon ba. Kuma kai da kanka ka shaida cewa zaben aka yi kuma su wa suka yi zaben? Ina ce su kansu ne ’yan majalisar suka yi zaben kuma suka zabi Aliyu Maduru? Abin da suka yi hakki ne da tsarin mulki ya ba su kuma shi suka zaba ya jagorance su. Sai me kuma?
Kila ko kana ganin cewa wai Maduru matashi ne dan shekara 32 ko? Amma kada ka mance ya cancanta, musamman ganin cewa yana da ilimi mai zurfi, wanda kai da kanka ka kawo bayanin cewa ya mallaki digiri har biyu. Idan batun karancin shekaru ne, kada ka mance, masana ilimin mulki sun yi bayanin cewa gwamnati mai inganci ita ce wadda ta kunshi dattijai da matasa. Don haka samun Dattijo kamar Masari a matsayin gwamna, da matashi kamar Maduru a matsayin Shugaban Majalisa, babban alheri ne ga Katsina da Katsinawa.
Bari in tambaye ka, Shin lokacin da su marigayi Matawalle Musa ’Yar’duwa da Galadima Nasir da dammasanin Kano suka zama ministoci a Gwamnatin Sardauna, ka san shekarunsu. Lokacin da Janar Yakubu Gowon ya zama Shugaban kasa, ka san shekarunsa? Shi ko auren fari ma bai yi ba a lokacin. Lokacin da Janar Murtala ya zama Shugaban kasa ko ka san shekarunsa? Shi kansa Shugaban kasa na yanzu, Muhammadu Buhari, lokacin da ya yi gwamna, ka san shekarunsa? Idan ba ka sani ba, dukkansu suna matasa ne masu jini a jika, suka rike wadannan muhimman mukamai; balle kuma Maduru da ya zama Shugaban Majalisar Jiha yana dan shekara 32?
Wannnan abin alfahari ne ga matasan Jihar Katsina da ma na Najeriya gaba daya, abin alfahari ne ga Shugaban kasa Buhari, saboda jiharsa ta fitar da matasa kunya.
Ina ba marubuci ko dan jarida danjuma Katsina shawarar cewa ya farka daga barci. Wannan gwamnatin ta Dallatu ba irin ta baya ba ce da za a ci ta da buguzun. Ba irin wacce za a yi wa barazana da karya ba ce, wai don a samu kafar shiga. Allah sa mu dace, amin!
Muhammadu Mustapha (08058538165), ya rubuto daga Mani, Jihar Katsina

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna