Martani: Kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A kwanakin baya ne muka kawo muku mukala a kan kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure. Wannan mukalar ta ja hankalin jama’a; maza da mata, inda suka rika turo sakonninsua a kanta. Saboda yadda ta dauki hankalin jama’a ne ya sanya muka ga […]

Martani: Kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure
Martani: Kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. A kwanakin baya ne muka kawo muku mukala a kan kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure. Wannan mukalar ta ja hankalin jama’a; maza da mata, inda suka rika turo sakonninsua a kanta. Saboda yadda ta dauki hankalin jama’a ne ya sanya muka ga dacewar sanya sakonnin da aka turo a kan ta.

Za mu fara da sakon Hajiya A’ishatu Abdullahi Nakelly, inda ya ce: “An yi sallah lafiya? yaya iyali? Da fatan duk suna cikin koshin lafiya. Kuma mun ga mukala kan kura-kuren da maza ke yi wajen zabar matar aure a filin Iyayen Giji. Allah Ya saka da Alheri.”
kanwar Maikawo daga Kano ta ce: “Assalamu alaikum, amincin Allah ya tabbata a gare ku. Ina yi muku fatan alheri. Da fatan kuna cikin koshin lafiya? Na ga mukalar da ka yi kan kura-kuren da mata suke yi wajen zabar miji da kuma wanda ka yi na kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure, kuma wallahi gaskiya ka fada. Abin da yake faruwa ke nan. Duk abin da ka fada gaskiya ne, shi ya sa za ka ga wasu matan suna kodar da jikinsu suna caba ado saboda samari. Yawancin matan da suke irin wannan dabi’a ba su da ilimin addini sai na boko. Ka huta lafiya.”
Sakon Nana Khadija daga Kano kuma cewa ya yi: “Assalamu alaikum, na ga rubutunka a jaridar Aminiya kuma na karu da shi. Ina yi maka fatan alkairi, Allah ya kara basira.”
Sakon Hamisu Ibrahim cewa ya yi: “Assalamu alaikum, barka da warhaka Malam Bashir, na ga mukalar da ka buga a filinka mai albarka, maza da mata kowa na tafka kura-kurai wajen zabar abokin zama. Abin da ya kamata a yi shi ne, kowane jinsi ya rika zabar abokin zama bisa doron gaskiya da kuma yadda addini ya yi umarni.”
Sakon Khalid Ibrahim cewa ya yi: “Assalamu alaikum, Malam Bashir Yaya aiki? Mukalar da kuka buga kan kura-kuren da maza suke yi wajen zabar matar aure tana jibge da darussa masu yawa. Fatana Allah Ya sa wadanda aka yi don su, su ci gajiyarta.”
dahiru Hussaini Makyakus (Dulmi): “Assalamu alaikum. Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya a kasarmu Najeriya. Na karanta mukalar kure-kuren da maza suke yi wajen zabar mata.”
Sule Harka daga Jihar Legas: “Assalamu alaikum. Na ga fadakarwar da ka yi wa maza da mata dangane da aure. Allah Ya saka da alheri, Ya sa ka gama lafiya, Ya kuma kare dukkan sharri. Allah Ya kara basira.”
Sakon B. Abubakar Abuja kuwa cewa ya yi: “Abin da ka fada haka yake babana. Matan yanzu sai a hankali, idan ka biye musu ba za ka aure su ba. To ni dai shawara nake nema a gare ka: Ni budurwata ta cika tambaya ta kudi, idan na nuna mata raina ya baci sai ta ce idan ba ta tambaye ni ba wa za ta tambaya, kuma ba ta damuwa da abin da ya same ni walau na farin ciki ko na bakin ciki, kuma ba ta yi mini kalaman soyayya, ba ta yin ko da tes na kauna da zai faranta mini rai, idan ka ga ta turo mini tes, to tana so ne ta tambaye ni kudi ko kuma ta ga na wuni ban kira ta ba. Da har na fara tunani ko na rabu da ita, amma tuni manyana sun riga sun yi magana da nata, har an ba ni ita. Na gode.”
Iyayen Giji: Kamata ya yi ka zauna da ita, sannan ka sanar da ita abubuwan da take yi maka wadanda ba ka so. Ka sanar da ita abubuwan da kake so ta rika yi maka. Allah Ya ba da sa’a.
S. Ubale Hadeja, Shugaban kungiyar Gizago na Jihar Jigawa cewa ya yi: “Wannan mako an ba ’yan mata da zawarawa kyakkyawar satar amsa. Allah Ya saka da alkairi. Da fatan Allah ya ganar da su.”
Khadijah daga Kano: “Assalamu alaikum, Malam Abubakar, Allah Ya saka da alheri. Cikin kura-kuren da mata suke yi ni ba na yin ko daya, amma idan na kira saurayina ba ya daga waya duk da ya san ba filashin nake yi masa ba, sai daga baya ya kira ni. Shin wannan ma karanta ce?
Abubakar Haruna daga Bauchi: “Assalamu alaikum, wallahi Malam Abubakar tun ranar da aka buga rubutun da ka yi kan kura-kuren da mata suke yi wajen zabar miji a jaridar Aminiya na shiga tashin hankali, saboda budurwata ta yi kememe cewa wai ni na yi rubutun don na ci mata mutunci. Har ta kai ga ta ce ta daina soyayya da ni. Na gaya mata cewa sunanmu ne ya zo daya, ban san ka ba, kuma ban taba ganinka ba amma ta ki yarda. Don Allah yaya zan yi?”
Iyayen Giji: Ka dauki wannan jarida, ka nuna mata labaran da nake turowa daga Legas, sannan ka nuna mata wannan amsar da na ba ka. Yake budurwar Abubakar, ki sani muna da wakili Abubakar Haruna daga Legas, ba Abubakar dinki na Bauchi ba ne ya yi rubutun da kike tuhumarsa a kan ya yi ne don ya ci mutuncinki.