Martani: Rasha ta sanya wa Amurka takunkumi
Martani ne ga takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka ta lafta wa Rashan.
Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar Rasha ta sanar da haramta wa shugaban Amurka Joe Biden da wasu manyan jami’ansa goma sha biyu shiga kasar.
Wannan dai wani mataki ne na mayar da martani ga takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka ta lafta wa Rashan.
Daga cikin manyan jami’an Amurkan da Rasha ta haramtawa shiga cikinta, har da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken da sakataren tsaro Lloyd Austin.
Har ila yau Rasha ta saka sunayen shugaban hafsan hafsoshin sojan Amurka Mark Milley da mai ba da shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan da daraktan hukumar leken asiri ta tsakiya William Burns da kuma Sakatariyar yada labaran fadar White House Jen Psaki cikin bakin kundinta.
A makon da ya gabata, Amurka ta haramta wa shugaban Rasha Vladimir Putin da Ministan Harkokin Wajen kasar Sergei Lavrov shiga cikinta, bayan lafta wa gwamnatin kasar ta Rasha takunkumin karya tattalin arziki, matakin da ya samu goyon bayan manyan kasashen yammacin Turai, saboda yakin da ta kaddamar kan Ukraine.
Biden zai gana da shugabannin NATO
Fadar White House ta sanar cewa ana sa ran Shugaba Joe Biden zai gana da shugabannin Tarayyar Turai da na Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO a Brussels a mako mai zuwa.
Tattaunawar ana sa ran za ta fi mayar da hankali kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, kuma batun da ake sa ran za su mayar da hankali sun kunshi batun tsaro da harakokin kasashe waje.
Shugaban na Amurka zai hadu da takwarorinsa na Turai a ranar Alhamis 24 ga watan Maris.