Martani: Tsakanin Tsintsiya da Lema

Yau kuma na ba masu karatun wannan shafi dama ne su tsoma bakinsu cikin wannan batu da muka tattauna a baya. Da fatar za a yi karatu lafiya. Bello Ahmadu Alkammawa: Allah Ya ci gaba da kasancewa tare da kai a dukkanin lamuranka, amin.Nuraddeen Nai: Malam ai kan mage ya waye, mu ma mun dade muna […]

Martani: Tsakanin Tsintsiya da Lema
Martani: Tsakanin Tsintsiya da Lema

Yau kuma na ba masu karatun wannan shafi dama ne su tsoma bakinsu cikin wannan batu da muka tattauna a baya. Da fatar za a yi karatu lafiya.
 
Bello Ahmadu Alkammawa: Allah Ya ci gaba da kasancewa tare da kai a dukkanin lamuranka, amin.
Nuraddeen Nai: Malam ai kan mage ya waye, mu ma mun dade muna tunanin hakan ganin cewa duk dai an gudu ne ba a tsira ba, domin duk wadannda suka bar mu muka sha rana, muka kuma jike sharkaf su ne suka dawo domin su share mu da tsintsinyar da suke ikirarin sabuwar sheka ce a gare su. Malam mun gode da sake fargar da mu da ka yi daga gyangyadin da muke yi.
Aminu Umar: Wannan batu gaskiya ne, ka yi tunani mai kyau, Allah Ya ba mu ikon fahimtar haka baki daya, don mu tsaya tare da jajircewa ga abin da zai kai mu ga ci gaban kasa.
Al-Ameen El-Jingi Abubakar: Hausawa na cewa karshen alewa kasa. Allah Ya sa tsintsiyar kuma ba ta sharar sauran kudaden ba ne zuwa asusun u…. Domin ai Hausawa na cewa kowane gauta ja ne sai dai in bai ji rana ba.
Abubakar Idris Dadiyata: Malam wannan shi ake kira tsaka-mai-wuya. Allah Ya kyauta.
Hassan Mohd  Malam, Mun gode.Wannan shi ake kira”rufin kan uwar dadi gabanta babu kariya.” Mu dai fatarmu Allah Ya kawo mana canji mafi alheri, Ya raba mu da ’yan handama da babakere.
Ibrahim Saleh Basawa: Malam muna tare da kai a kowane lokaci, Allah Ya sa wadanda aka yi don su, su gyara.
Bash Twins: Lallai kukan kurciya ma jawabi ne mai hankali ke ganewa, kuma da alama in ganga ta faye zaki fashewa za ta yi. Malam godiya muke, Shawara dai ta rage ga mai shiga rijiya.
Yahya Umar Usman: Malam Ibrahim ya kamata a buga wannan rubutu domin kara wayar da kan al’umma kuma muna rokon Allah Ya kara maka tsawon rai mai amfani, Allah Ya kara basira.
Bashar Abdu: Allah Ya kara wa Malam lafiya, wannan batu haka yake, kuma Malam mafita za a dora jama’a a kai, saboda jagwalgwalon da ke cikin tsintsiyar ba karamin sabulu ne zai wanke shi ba. Amma da za mu dauki manofofin Malam Aminu to da canjin ya samu, to yanzu Malam ina mafita?
Bello Usman: Allah Ya kara wa Malam lafiya da hazaka, wallahi muna godiya da wannan tunatarwa da ka yi mana. Allah Ya kara basira da tsawon rai.
Ibrahim dalhat: Hausawa na cewa wai da kamar wuya gurguwa da auren nesa. Mun wayi gari a kasar nan inda mulki ya zama jalli-joga (ba a rabu da Bukar ba an haifi Habu)….Na dade ina tunanin wannan canja sheka da ’yan Lema suke yi zuwa Tsintsiya amma fa manufofinsu ba wai canjawa suke ba. Abin da ke zucinsu yana nan. Hausawa sun ce mahaukaci ba ya warkewa sai dai ya ji sauki…..kiranmu ga al’umma shi ne mu hankalta, kada mu sake aukawa cikin tsaka-mai-wuya……Malam mun gode da jan hankula, Allah kara lafiya da basira Ya kuma saka da alheri…Amin
Salisu Suleiman dan’Nasarawa: Malam! Ai tun yanzu ire-iren wadannan haurobiyawan, wato ’yan canjin sheka sun fara nuna halin nasu, wanda kada’an na nuna wa jama’a cewa su ba wai burinsu ba ne a samu sauyin rayuwa. A a, maimakon haka burinsu kawai shi ne yaya za su yi su sake hayewa kan karagar mulkin jama’a da kuma ci gaba da danne jama’a su da ’ya’yansu. Ba wai yaya za a yi a taimaka wa talakawa ba. Idan mun dubi ma’anar ita kanta kalmar dimokurdiyyar za mu fahimci cewa ba an yi ta ba ne don wasu kebabbun mutane ba. Domin kuwa ma’anar na cewa ne gwamnatin jama’a, wadda jama’a ta zaba, domin jama’a. Saboda haka ya kamata talakawa su yi karatun ta-natsu domin ganin cewa an saka sabuwar sheka wadda ba mu hada ta da lalatacciyar tsohuwar ciyawa ba, domin kuwa hakan zai iya ba mu damar ganin cewa sabuwar shekar ta yi nagarta da kuma karko. A nan ina son in yi amafani da wannan dama domin in yi kira ga talakawan Najeriya cewa ya kamata a lura da bara-gurbi, wadanda burinsu kawai shi ne su samu dama su yi amfani da talakawa domin cimma burinsu, su kuma in ya so su mutu ba matsalarsu ba ce.
Rufa’i Surajo: Allah Ya gafarta Malam, wadannan batutuwa duka gaskiya ne, kuma wannan ya zama kalubale ga talakawa da su himmatu wajen duba shugabannin da suka dace su zaba.
Abubakar Lawal: Allah Ya sa mu hankalta da wadannan kyawawan bayanan na wannan Shehun Malami, kuma Allah Ya kare Malam da mu daga sharri.
Nazir Adam Salih: An gaishe da Shehin Malami, wallahi ka fadi abin da ke raina kullum na kasa amayar da shi.
Nazir Ibrahim Abbas: Gaskiya ne Allah gafarta Malam, na dade ina tunanin matsalar kasar nan ba ta jam’iyya ba ce, sai dai shugabanni nagari domin akwai wadanda za su labe ga jam’iyyar kuma ba mutanen kirki ba ne, da wannan canja shekar daga lema zuwa tsintsiya sai ina ganin wata sabuwar lemar ce kawai za a yi. Masu iya magana sun ce mene ne bambancin dambe da fada? Ya kamata al’umma su fahimci inda aka dosa.
Zaharadden Nasir: Gaskiya wannan batun shi ya kamata a ce dukkan mahankalta sun nazarta.
Salisu Maladi Darazo: Gaskiyarka Malam mai tsage gaskiya, komai labewarta, mai fito da ita duk inda ta shiga.
Murtala Isa: Allah Ya kara wa Malam basira da hikima, Allah Ya kara maka lafiya da fasaha. Mun gode da fadakarwa.
Sulaiman Usman: Malam Allah Ya saka da alheri, kuma Ya sa hakan shi ne mafi alheri a gare mu da wannan kasa tamu.