MARTANI: Yara ’ya’yan kowa ne?

Yau ma kamar makon da ya wuce na bai wa masu biye da mu a cikin wannan shafi a Intanet damar tofa albarkacin bakinsu kan rubutun da na yi kan kULAFUCIN IYAYE GA ’YA’YA, da fatar za mu sha karatu lafiya. Chiroma Hadi Khan Jallo: Malam, lamarin akwai abin dubawa, gurbacewar zumunci ne ya haddasa […]

MARTANI: Yara ’ya’yan kowa ne?
MARTANI: Yara ’ya’yan kowa ne?

Yau ma kamar makon da ya wuce na bai wa masu biye da mu a cikin wannan shafi a Intanet damar tofa albarkacin bakinsu kan rubutun da na yi kan kULAFUCIN IYAYE GA ’YA’YA, da fatar za mu sha karatu lafiya.

Chiroma Hadi Khan Jallo: Malam, lamarin akwai abin dubawa, gurbacewar zumunci ne ya haddasa wadannan matsalolin.
Sunusi Tijjani Kwari: Hmmm! Malam hakika rayuwar yanzu tana bukatar gyara, domin wannan bayani naka akwai abin lura kwarai kam. Allah Ya kara basira.
Mustapha dankano: Malam Ibrahim wannan lamari ya fi faruwa a kan Bahaushe wanda ka riga ka fadi, kuma wallahi kashe kanmu muke yi. A ce wai ba za ka taimaka wa dan kanenka ba, ko wanka ko makwabcinka, domin kada ya zama wani abu. To abin da Allahu Ya kaddara ba ka iya canza shi ko ka taimaka ko ba ka taimaka ba, sai ya zama abin da Allah Yake so. Shi ya sa da Malam Bahaushe ya aje aiki ka ba ya shekara biyu, sai ya zama abin tausayi, domin wanda ya kamata ya taimaka bai taimake su ba. Allah Ya shirya halin Bahaushe, Ya kuma sa mu dace, amin.
Abdullah Arzika Jaredi: Malam ka tsunduma ni kogin tunani. Ka tuna mini da tawa rayuwar. Ba zan manta da rasuwar mahaifina ba, tun ban kammala firamare ba, hakan ya sa na fada gararamba, har ’yan uwana suka gama makaranta ban da mai taimakona. Sai da na samu wani mai tunani irin naka mai suna Abdullahi Yabo wanda ba zan taba mantawa da shi ba, ya yi tattalina don ganin na zama mutum nagari. Bisa hakan ne ya nemi izinin mahaifiyata, kuma ta ba shi don ci ci gaba da karatuna. Wallahi Malam yau sanadiyarsa ina da shaidar kammala sakandare da NCE da kuma digiri, duk ta dalilinsa. Allah abin godiya.
Baba Sama’ila Lamarin da ban tsoro sai ka ga danka na harararka kuma fa kai ka haife shi a jininka. Allah Ya kyauta.
Lawan Muhammad PRP: Malam muna sauraren kuma irin wannan tsokacin a kan uba ma uban kowa ne. Allah Ya saka da alheri.
Kamal Y. Iyantama: Ikon Allah! Haka ne wannan. Sannu Malam.
Hafiz Koza Adamu: Hakika da za a samu hakan a cikin daukacin al’umarmu, to da an yi rayuwa ta sa’ada da ganin girman juna.
Kodayake ya kamata kowa ya dauki da a matsayin dansa, haka ma ya kyautu kowa ya kalli uba a matsayin ubansa; ni dai daga wannan darasi na Malam, na kara hakkakewa cewa ina da iyaye ba adadi a wannan rayuwa. Allah kara wa Malam lafiya da gabata! Mun gode!
Lawal Ibahim Tanimu: Babu shakka irin wannan mugun tunani ne a fahimtata ya zama kanwa uwar gami wajen ruda halin zamantakewa a kasar nan. Abin bakin ciki shi ne, kamar yadda Malam ka misalta, akwai wadansu ’ya’ya a nan kasar da ba diyan kowa ba ne, amma aka samu wasu masu tunanin ganin cewa lallai da na kowa ne suka mayar da wadancan diya kamar nasu, har suka zama abin da suka zama, amma duk da wannan gata da suka samu sai kawai suka yi godiyar maye. A sakamakon haka, sai kowa ya fara tunanin aiki da muguwar karin maganar nan ta Hausa mai cewa wai “idan ka ga mutum a rana, kawai ka kara tura shi ciki.” A ganina wannan mummunan tunani ne, kuma har sai mun canza shi kafin mu fita daga cikin manyan matsalolin zamantakewa da ke addabarmu. Allah Ya kyauta kuma Ya saka wa Malam Malumfashi Ibrahim da mafificin alheri.
Rayyan Ibrahim: Allah Ya saka da alheri Malam, ya sa mu fi karfin zukatanmu.
Abban Ammar Elmusa Usman: Allah Ya gafarta wa Abubakar Gimba, kamar ya yi rubutu a kan hakan ko in ce game da rayuwarsa ta farkon fari. Abin da ban tsoro.
Aminu Kabir: Allah Ya saka da alheri, irin wannan fadakarwar ita ya kamata Malaman addini su rika yi!
Sada Bin Suleiman Usman: Tabbas da kowa zai kasance irinka, wallahi da duniyar ma ba ta zauna cikin rikici da halin ha’u’la’i ba!
Abdulkareem Raubilu: Tabbas wannan nasiha ta nasihantar, sai dai fatar Allah ya ba da ikon aiki da ita kai kuma ya kara ma lafiya da basira.
Sani Ahmad Sagagi: Malam rayuwar Bahaushe cike take da abubuwan mamaki da bai fiye damuwa da su ba. Sai kuma ruwa ya ci shi ya fara neman ina mafita. Irin wadannan matsaloli ke haifar da yawaitar batagari a cikin al’umma daga karshe su rika karewa a kan masu ikon da suka kasa tallafar su. Saboda haka fadakarwa ce da kowa ya kamata ya duba kansa da wanda ke tare da shi.
Bello Agala: Gaskiya ne adabi tumbin giwa ne kuma ruwan zafi ne wanda ba ya da gefe, domin adabi ya tabo ko’ina, musamman idan muka yi la’akari da wannan bakandamiyar nasihar ta Malam. Allah Ya saka da alheri.
Bilkisu Sulaiman Abdul: Allah Ya saka Malam.
Hassan Mu’azu Fago: Allah Ya saka da alheri.
Muhammad Auwal Badaru: Ba abin da wannan tunanin na kulafucin ’ya’ya zai amfana mana. Kuma ba ko tantama wannan gaskiya ne, sai dai kamar koyaushe al’adar gaskiyar ita ce zamantowa mai daci da ganci ga kunnen mai saurare. Ina ma za mu daure mu karba hannu bibbiyu!
Akilu Lawal dangamau: Allah Ya sa mu gane.
Ismail Idi Yari: Haka ne, amma kuma shi Malam Bahaushe da kansa, yana cewa “Ka so naka, duniya ta ki shi, ka ki shi kuma duniya ta so shi.” Don haka kukan kurciya….
Al-Mansoor Gusau: To! Ku malamai, sai ku yi kokari ku ci gaba da koyar da al’umma tarbiyya. Allah Ya saka Malam.