Martanin mutane kan tallafin Rahama Sadau da Hassan Giggs ga almajirai

Shigowar sanyi a mako biyu da suka gabata a nan Arewa ya sa Jaruma Rahama Sadau da Furodusa kuma Darakta Hassan Giggs sun tallafa wa almajirai da kayan sanyi a jihohin Kaduna da Kano Jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram da Facebook cewa, “Mun zagaya jiya. Da dama daga cikin almajiran sun yi barci […]

Martanin mutane kan tallafin Rahama Sadau da Hassan Giggs ga almajirai

Shigowar sanyi a mako biyu da suka gabata a nan Arewa ya sa Jaruma Rahama Sadau da Furodusa kuma Darakta Hassan Giggs sun tallafa wa almajirai da kayan sanyi a jihohin Kaduna da Kano

Jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram da Facebook cewa, “Mun zagaya jiya. Da dama daga cikin almajiran sun yi barci cikin natsuwa. Muna godiya ga wadanda suka bayar da gudunmawa. Allah Ya saka. Yanzu muka fara,” inji ta.

A makon jiya ne jarumar ta wallafa a shafukan nata cewa tana neman tallafin kayan sanyi domin tallafa wa almajirai a karkashin Gidauniyar Ray of Hope, inda ta ce, “Bai kamata a yi watsi da almajiran ba. Iska daya muke shaka. Ya kamata mu hada hannu wajen taimakon almajiran nan fisabilillah. Mu taimaka musu da riguna a wannan lokaci. Ina bukatar mutum shida: Ali Jita da Hadiza Gabon da Adam A. Zango da Umar M. Shareef da Sadik Sani Sadik su yi amfani da damarsu wajen isar da sakon nan kuma su taimaka. Kai ma za ka iya neman abokinka ya taimaka wajen bayar da gudunmawa ko yada bukatar nan.”

A Jihar Kano, Hassan Giggs ya kai wa amajiran daukin kayan sanyi domin samun saukin sanyin da ya kunno kai a kwanakin da suka wuce.

Hassan Giggs ya raba kayan ne a makarantun allo da dama a unguwanni da yawa na cikin birnin Kano.

Hassan Giggs ya ce ya tallafa wa almajiran da kayan sanyin ne bayan ganin wadansu daga cikinsu da ya yi suna fama da matsanancin sanyi.

“Gaskiya kasancewar mun lura da yadda suke rayuwa cikin kunci  a wannan lokaci na sanyi, ya sa muka yi tunanin taimaka musu da kayan sanyin. Na lura cewa da yawansu ba su da kayan sakawa masu kyau, wasu ko takalma ba su da su. Idan ka auna za ka ga yaya mutum zai kasance ba tare da wadannan muhimman abubuwa ba.

Ya ce da ya lura da haka ne, sai ya kira abokinsa Ali Jita ya ce masa ya kamata su yi wani abu game da haka domin taimakon wadannan yaran da suke kwana a kan titi. Daga nan sai ya yi kira ga iyaye su dage wajen daukar nauyin da Allah Ya dora musu, sannan ya bukaci su saya wa yaransu duk abubuwan da suke bukata kafin su tura su makarantu.

Sai dai bayar da tallafin ya jawo cece-ku-ce a dandalin sada zumunta na facebook da Instagram inda wadansu suke yabo wadansu kuma suke suka, musamman ga Rahama Sadau. Aminiya ta tattaro wasu daga ciki kamar haka:

A shafin Facebook wani mai suna Muhd Al-ameen Drn cewa ya yi kan Rahama Sadau: “Alhamdulillah kan kirkiro wannan shiri. Wannan babban kalubale ga mutane musamman masu dukiya saboda kowane mutum yana da dama, kuma yana da kyau gare shi ya taimaki talakawa. Ina yi miki addu’a Allah Ya sanya wannan shiri ya zamo hanyarki ta zuwa Aljanna.”

Shi kuwa Sabiu Hussaini cewa ya yi: “Masha Allah alhamdulillah, Allah Ya kara karfafa miki gwiwa ki ci gaba da aikin alheri irin wannan na taimakon al’umma kuma Allah Ya kara daukaka ki Ya rabaki da sharrin makiya da mahassada, Rahama Sadau ikon Allah!”

Shi kuwa Kwamared Shafeeu Bello Idris Kaura-Namoda cewa ya yi cikin Ingilishi: “Mun gode miki. Kin yi aikin kwarai. To amma ki tuna ya kamata ki yi aure tare da kauce wa duk abin da ba ya da kyau kamar bayyana hotunan surar jikinki da sauransu. Allah Ya yi miki rahama ke da sauransu.. Allahummah Yashfeekee. ’Yar uwa”

Sai Agt Rabiaturraayi Rabiu Sakafa Malam Abdullahi Yahaya da Malam Sirajo Ladan suka ce: “Abin jin dadi! A lokacin da wadansu suke suka da watsi da tsarin almajirancinmu, sai ga wadansu suna kokarin tallafa musu. ALLAH YA ALBARKACI RAYUWANKI @Sadau”

Shi kuwa Abubakar Mustapha Kiru cewa ya yi: “Masha Allah! Wannan babban taimako ne. Sun cancanci a nuna musu soyayya da kula a kuma girmama su. Za mu ci gaba ne kawai idan muka koyi bayar da tallafi ga wadansu. Godiya gare ki kan bullo da wannan muhimmin shiri. Kuma ina da tabbacin zai samu nasara, saboda hannunki hannun zinari ne, duk abin da kia taba zai yi albarka. Allah Ya albarkaci wannan shiri Ya daukaka shi.#Gracias #Sadauzhomeonthespotlight #almajirimutum

Sai Abdulmumin Ibrahim Jega da ya ce: “Ki ci gaba Sadau, bayaninki na yau ya yi matukar sanya min farin ciki.”

Yusuf Naseer Dogo Jega kuwa cewa ya yi: “Wannan Hajiyar tamu ta cancanci yabo kan wannan aikin kwarai. Yau kam an yi abin kwarai !”

Shi kuwa Alhaji Abdul Benzy cewa ya yi: “Ke dai ga ki ’yar duniya ga son taimako. Allah Ya kyautata karshenmu gaba daya.”

Amma shi kuwa Abubakar Sadeek ya yi wa shirin kallo na daban ne, inda ya ce: “Hmmm ku ga kasuwanci… wannan wata hanya ce ta samun KUDI.”

Ibrahim Idris Maru kuma cewa ya yi “Rahma yau kin burge ni Allah Ya kara shirya ki Ya kuma shirya mu. Allah bada lada.” Yayin da Adam Lica Frosh ya ce: “Kamar gaske…. Allah Ya sa ba neman yabo ba ne.”

Abubakar Haruna Rasheed kuma cewa ya yi: “Kin yi kokari, da ana ta zaginki ashe kin fi wadansu masu zagin naki amfani.”

Daga cikin wadanda suka mayar da martanin, wani mai suna prince_khalip_sadau a Instagram ya ce, “Allah Ya kara arziki Hajiya.”

Shi ma harunachper cewa ya yi, “Allahu Akbar! Muna godiya sosai Didi.” Sannan wani mai suna i_am_dan_sada ya ce, “Allah Ya bayar da lada.”

Shi kuma wani mai suna abacha7126 cewa ya yi, “Yaya batun ’yan gudun hijira kuma? Ku ’yan Kannywood ba ku yi komai ba game da ’yan gudun hijira, kuma ya kamata ku tuna cewa kuna da masoya da yawa a cikinsu.”

A nata martanin, wata mai suna elrash_ cewa ta yi, “Don Allah a daina kiran sunan mutum, domin riya tana bata aiki. Daidai take da shirka.”

Shi ma wani mai suna balarabe_muhd_buhari cewa ya yi, “Allah kamar yadda bayinKa suka taimaka wa wadannan yara, Ya Allah Ka bude musu kofofin Aljanna, amin. Mu ma Allah Ka ba mu ikon taimakawa, amin.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50