Martinez ya zama sabon kocin Portugal
Martinez ya ajiye wa Belgium aiki bayan gaza tabuka komai a Gasar Kofin Duniya.
Tsohon mai horas da tawagar ’yan wasan kasar Belgium, Roberto Martinez, ya zama sabon kocin kasar Portugal.
Martinez ya maye gurbin Fernando Santos wanda Hukumar Kwallon Kafar kasar Portugal ta sallama bayan rashin nasara a hannun Maroko a matakin Kwata-Fainal a Gasar Kofin Duniya da aka gudanar a Qatar a 2022.
- NAJERIYA A YAU: Ma’aikatar Shari’a ta fadi gwajin tsare gaskiya —ICPC
- Hatsari ya ci mutum 2, wasu 5 sun jikkata a hanyar Abuja-Kaduna
Kocin, dan asalin kasar Sifaniya, ya samu kalubale a Gasar Kofin Duniya, inda Belgium ta gaza fitowa daga Matakin Rukuni, lamarin da ya sanya ya yi murabus daga matsayinsa.
Belgium ta fito a rukuni daya da Kanada, Maroko da kuma Croatia amma ta gaza yin katabus.
Babban kalubalen Martinez a yanzu shi ne kai Portugal ga nasara a Gasar Nahiyar Turai da za a yi a 2024 a Kasar Jamus.