Marubuta a Najeriya, Masu Karatu a Nijar: Nazari a kan bukatuwar jaridun Hausa a Kudancin Nijar
An gabatar da wannan takarda ce a taron kara wa juna sani mai taken ‘Maradi Kwalliya’ a jeren shirye-shiryen bikin tunawa da ranar samun ’yancin Jamhuriyar Nijar, wanda aka yi a ranakun 14 zuwa 16 ga watan Disamba 2015 a Jihar Maradi, Jamhuriyar Nijar. Gabatarwa: A kasashen da ake da jama’a masu amfani da […]
An gabatar da wannan takarda ce a taron kara wa juna sani mai taken ‘Maradi Kwalliya’ a jeren shirye-shiryen bikin tunawa da ranar samun ’yancin Jamhuriyar Nijar, wanda aka yi a ranakun 14 zuwa 16 ga watan Disamba 2015 a Jihar Maradi, Jamhuriyar Nijar.
Gabatarwa: A kasashen da ake da jama’a masu amfani da harshen Hausa a ko’ina a duniya, babu wadanda suka kai kasashen Najeriya da Nijar, wadanda suka hada iyaka mai tsawon kilomita 1,500 (mil 930), baya ga kasancewar mutanen yankin al’umma daya tun lokaci mai tsawo. A wadannan kasashe da sauran ire-irensu, inda harshen Hausa yake harshen sadarwa da zamantakewa, babu wata kasa da Turawan Yamma suka yanka wadda take ta Hausawa ce zalla, mai amfani da harshe daya, misali Hausa zalla, wanda yin hakan ba zai bai wa ’yan mulkin mallakar damar yada nasu harshen wajen koyarwa ko sadarwa, kai har ma karbuwa ga jama’ar ba, domin ba za a samu bukatar amfani da wani harshe ba, kasancewar kowa yana jin abin da dan uwansa yake fadi.
Duk da kasancewar wadannan kasashe da aka yi wa mulkin mallaka hadaka ne na harsuna daban-daban amma Hausa ba ta rasa samun muhimmanci daga wadannan kasashen mulkin mallaka ba, har zuwa yanzu. Kasashe irin su Faransa da Ingila da Jamus da Amurka har da kasashen da suka taso a yanzu irin su China, duka suna da kafafen watsa labarai da suka dauki wani bangare na yau da kullum da suke watsa labarai da sauran shirye-shirye ga duniya cikin harshen Hausa.
Amma duk da haka babu wata kasa da ake magana da harshen Hausa da take da jarida ta Hausa wadda take fitowa kullum (zuwa shekarar 2015), sabanin na Ingilishi ko Faransanci. Wannan matsala ta rashin wadatar kafofin watsa labarai cikin harshen Hausa, musamman a janibin (bangaren) rubutattun hanyoyi, shi ne abin da wannan takardar take son ta yi bayani a kai, domin a yi tsokaci da samar da hanyar wanzuwar irin wadannan ayyuka na adabi a kafafen watsa labarai na rubutu cikin Hausa. A bisa wannan dalilin ne ya sa wannan makala ta yi kokarin binciko dalilin da ya kawo kamfar jaridu da mujallun Hausa, a kasashen da mafi yawan mutanen kasar suna ji kuma suna magana da harshen Hausa, musamman Najeriya da Nijar. Shin ina matsalar take? Wannan takarda za ta amsa wadannan tambayoyi, domin samun bakin zaren warware matsalar.
Kayan aiki da hanyar bincike
Hanyar da aka bi domin gudanar da wannan bincike ita ce ta yin nazarin wasu ayyukan da suka gabata a kan tsantsar aikin jarida a kasashen biyu. Bayan wannan hanya ta biyu da aka bi wajen gudanar da wannan bincike ita ce ta yin hira da mutanen da suke cikin aikin jarida a Nijar da Najeriya. Kayan aikin sun hada da jaridu da mujallu da dokoki da littattafai da mukalu na tarurruka da na cikin intanet.
Mece ce jarida?
Kalmomin ‘jarida’ da ‘mujalla’ asalinsu kalmomin Larabci ne, wadanda suke nufin labarai da bayanai wadanda ake rubutawa ko ake bugawa cikin warkokin takardu, su fito da wani tsayayyen suna da aka ba jaridar ko mujallar a wani kayyadajjen lokaci, amma a jere-a-jere, misali kullum-kullum, ko mako-mako, ko sau biyu a wata, ko a wata-wata, ko sau hudu a shekara, ko kuma a shekara-shekara (Yahaya, 1988:141).
Manufofin kafa kafafen watsa labarai
Kowace kafar watsa labarai aka samar da ita, babu shakka akwai wasu manufofi a cikin wannan kafawar, sai dai kowa da irin tasa akidar ko manufa da ta sanya ya kafa wannan waje. Don haka jarida ma in an kafa ta ana sa ran wanda ko wadanda suka kafa ta, suna da tasu manufar.
A Amurka tun 1966 suka fara gwada karfin kafafen yada labarai wajen watsa manufa. Sun yi wannan ne a lokacin zaben Shugaban Kasa, inda suka samu cewa bukatun da mutane suke bayyanawa suna da alaka da abin da kafafen watsa labarai suke yadawa. An yi irin wannan a Japan a 1986, Ajentina a 1997, Mujallar The Times a Ingila su ma sun gudanar da irin wannan bincike, kuma dukan sakamakon da suka samu yana nuni ne a kan tasirin manufofin kafafen watsa labarai ga ra’ayoyin jama’a. (McCombs, ba kwanan wata: 3-5).
Tarihin samuwar jaridun Hausa a kasashen Nijar da Najeriya
Aikin samar da jaridu da mujallun Hausa a wadannan kasashe biyu ya samu ne a cikin karni na 20. Jaridar Hausa ta farko da aka fara bugawa a Arewacin Najeriya, ta samu ne a 1932, wannan jarida ita ce ‘Jaridar Najeriya ta Arewa’ (Gidan Dabino, 2011). Garba S. A. (2014), a wani nazari da ya yi a kan jaridun Hausa a Jamhuriyar Najar, ya kawo tarihin samuwar jaridun Hausa a Jamhuriyar Nijar, Garba ya bayyana cewa:
“Ba a fara tsara jarida ana bugawa da wani harshen kasar Nijar ba sai da tsakiyar karni na ashirin ya gota. Domin kyautata koyar da ilimin yaki da jahilci da wayar da kai, Ma’aikatar Yaki da Jahilci ta kasa ce ta fara buga jarida a cikin harshen Hausa da wasu harsuna don larduna/yankunan kasar, domin su samar da abin koyon karatu a makarantu ga daliban yaki da jahilci. Jaridar Sabon Ra’ayi da ta fito a 1963 ce jaridar farko (ta Hausa) da aka samar a Jamhuriyar Nijar.”
Wannan ya nuna cewa an fara samar da jarida cikin harshen Hausa a Najeriya da Nijar a cikin karni na 20, duk da cewa an samu kimanin shekara 31 da fara buga jaridar Hausa a Najeriya kafin a fara samar da ita a kasar Nijar. Yanzu muna cikin karni na 21 amma duk da haka, za a iya cewa halin da jaridun Hausa suka shiga, musamman a Nijar abin takaici ne, kasancewar an haura sama da rabin karni da fara samar da jaridar Hausa amma a ce har yanzu ba a samu ta tsaya ba. Baya ga rashin samun dorarriyar jarida, har yanzu an kasa samar da jaridun Hausa da suka amsa sunan jarida kamar yadda ake da su a sauran harsuna, domin girma da fadi da yawan shafukan jaridun Hausa na Nijar ba su kai yadda za a kira su jarida ba.
Dalilin karancin jaridun Hausa a Nijar: An bar jaki ana dukan taiki
Duk da yawan harsunan da ake da su a kasar Nijar kamar irin su Buduma da Fulfulde da Gulmacema da Kanuri da Larabci da Tamashek (Buzanci) da Tubanci (Tubu) da Zarma amma dukansu idan aka hada su, ba su kai yawan mutanen da suke yin amfani da Hausa ba, domin Hausa ita ce take da kashi 55.36 cikin 100 na adadin Hausawa na asali. Baya ga wannan, Garba (2014) ya kawo wasu nazarce-nazarce da Powel (2012) da kuma Wolff (1991) suka yi. Duka wadannan suna nuna cewa fiye da kashi 70 cikin ko 80 cikin 100 na al’ummar Nijar sun dogara a kan harshen Hausa a matsayin harshen hulda. Wannan ya isa hujja ga gwamnati da masu hannu da shuni su samar da wannan kafa ta wayar da kai da ilimantar da juna a cikin rubutun Hausa musamman ta hanyar jarida.
Dalilai da dama sun haifar da dakushewar jaridun Hausa a Jamhuriyar Nijar, amma manyan matsalolin da suka kawo hakan su ne rashin jajircewa da amfani da dabarun kasuwanci yadda ya kamata. Yawa-yawan masu ruwa- da-tsaki a kan aikin jarida a Nijar sun tafi a kan cewa gwamnati da Turawan mulkin mallaka su ne tushen dakile jaridun Hausa. Daga cikin irin wadannan mutane akwai Sule Maje Rejeto wanda ya bayyana cewa:
“Abin farko da ya kawo karancin aikin adabin Hausa a Nijar shi ne rashin ma’ilimantan adabin a cikin harshen Hausa. Na biyu shi ne, duk kokarin da Jami’ar Yamai take yi a fannin harsuna cikin harshen Faransanci take yin sa. Na uku ba a fitar da daliban ilimin Hausa sak, balantana su shiga bincike da neman ilimin adabin Hausar a cikin Hausa. Sannan na hudu, ba sashen koyar da ilimin harshen Hausa a jami’a. Duk adabin da mutane suke rayawa da Faransanci ne.” (Tattaunawa, 10 ga Nuwamba 2015).
Haka nan Salisu Isa Rediyo Garkuwa ya kara da cewar, akwai tsarin koyar da harsuna a Nijar, bai ba da damar zurfafa ilimin harsunan gida ba daga firamare shi ke nan. Ya kara da cewa: “Wadansu ma na daukar karatu da rubutu (da Hausa) tamkar kauyanci ne.” (Tattaunawa, 4 ga Nuwamba 2015). Sauran mutanen irin su Nuhou Jangwarzo duk sun tafi a kan wannan ra’ayin, kamar yadda yake cewa: “Harsunan gida ba su da muhimmanci a wajen hukuma da ’yan kasa. Idan ka sa manyan kaya (doguwar riga da hula) kuma ba ka Faransanci, to babu mai daukar ka da daraja. Sai ko idan an san ka tun da.” (Tattaunawa, 5 ga Nuwamba 2015). Daga cikin wadannan dalilai akwai maganar irin kallon da wadansu manyan ’yan boko suke yi cewa karanta jaridar Hausa sai marasa zurfin ilimi ko ’yan yaki da jahilci, saboda mamayewar da Faransanci ya yi.
Amma abubuwa da yawa sun yi nuni kan cewa jaridar Hausa za ta taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi da shigar da manufofin gwamnati da na kungiyoyi da sauran jama’a. Isa Danmusa, a tattaunawar da muka yi da shi, ya bayyana muhimman dalilai da suke nuni a kan haka, kamar yadda yake cewa:
“Ni shaida ne game da wadansu manyan mutane a kasar Nijar da suke son karatun jaridar Hausa da kuma yin hira cikin harshen Hausa, kamar Sunusi Tambari Jaku (ba Bahaushe ne ba) da tsohon Shugaban Nijar, Tandja Mahammadu (ba Bahaushe ne ba) da Bazun Muhammad tsohon Ministan Harkokin Kasashen Waje (ba Bahaushe ne ba), duk wadannan mutane suna son karanta jaridar Hausa da kuma yin hira cikin harshen Hausa. Ayyukan adabin Hausa sun taimaki wadansu mutane wajen harkar aikinsu. Misali, Tile Amadu, wadda ta taba gaya min cewa, sauraro da kuma karance-karancen ayyukan adabin Hausa (jaridu da littattafai) ne suka sa ta iya karatun Hausa, wadda ita ba Bahaushiya ba ce, amma sai da ta zama shugabar shirye-shirye ta gidan Rediyon Nomad FM da ke Agadez, sannan ta je Sashen Hausa na gidan Rediyon DW a Jamus ta yi aiki. Yanzu haka kuma ita ce wakiliyar DW a Abidjan ta kasar Kwaddibuwa.”
Wannan irin sha’awa ta amfani da jaridun Hausa ta dade tana wadari a cikin Nijar, domin Abdullahi Jori Hamani dan marigayi tsohon Shugaban Nijar, Jore Hamani, ya ce: “Mahaifina yana son karanta jaridun Hausa, domin lokacin da sojoji suka yi masa juyin mulki, aka tsare shi a gidan kaso, cikin abubuwan da ya nemi a rika kawo masa akwai jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo da ake bugawa a Najeriya.” Wannan akidar ita Abdullahi Jori Hammani ya ci gaba da rayuwa bisanta, shi ma yana karanta jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo kuma yana son ya yi hira da jaridar, har ya koma ga Allah. (Danmusa, 2015).