Marubuta Labarin wasanni sun karrama Drogba
Kocin Chelsea na Ingila Jose Mourinho ya bayyana Didier Drogba a matsayin dan kwallon da ba a taba yin kamarsa a kulob din Chelsea ba. Kocin ya bayyana haka ne a bikin karramawar da kungiyar Marubuta Labarin Wasanni na Ingila ta yi wa Didier Drogba a karshen makon jiya.Bikin karramawar ya gudana ne a Otel […]
Kocin Chelsea na Ingila Jose Mourinho ya bayyana Didier Drogba a matsayin dan kwallon da ba a taba yin kamarsa a kulob din Chelsea ba.
Kocin ya bayyana haka ne a bikin karramawar da kungiyar Marubuta Labarin Wasanni na Ingila ta yi wa Didier Drogba a karshen makon jiya.
Bikin karramawar ya gudana ne a Otel din Saboy na Lanadan a ranar Lahadi 25 ga watan nan da muke ciki.
Mourinho ya ce ya zabi ya jinjinawa Drogba ne a matsayin dan kwallon da babu kamarsa a kulob din Chelsea ganin yadda ya kawo cigaba a gasar rukunin firimiya ta Ingila tun daga lokacin da ya fara yi wa kulob din Chelsea na Ingila wasa kawo yanzu.
Kocin ya bayyana Drogba a matsayin “Gwarzon da babu kamarsa a kulob din Chelsea”.
“Tun lokacin da na fara aikin horarwa ban taba bayyana wani dan kwallo a matsayin wanda na fi yarda da shi ba sai a wannan karo da na zabi Drogba a masayin Gwarzon dan kwallona, kuma a gaskiya ya cancanci yabo. Tun lokacin da Drogba ya fara yi wa Chelsea wasa, ya kawo canji da kuma kalubale a gasar rukunin firimiya don haka na zabe shi a Matsayin Gwarzon dan kwallon Chelsea”, inji Mourinho.
A nasa jawabin, Drogba ya bayyana matukar farin cikinsa game da karramawar da kungiyar marubuta labarin wasanni ta Ingila ta yi masa a wannan lokaci. Kuma ya sha alwashin cigaba da yin kokari har lokacin da zai yi ritaya daga yin wasan kwallon kafa.
kungiyar dai tana gudanar da karrama ’yan kwallon da suka shahara ne a bikin da take shiryawa a kowace shekara.