Marubutan Hausa sun nemi a tashi tsaye wajen tallafa wa harshen

Gabatarwa: Gamayyar kungiyoyin marubuta kagaggun labarai na fadin Najeriya da sauran kasashen da suke amfani da Hausa a fadin Afirika ta Yamma,   sun gudanar da Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya wanda shi ne irinsa na farko.An yi wannan taro ne daga ranar Asabar 26 zuwa Lahadi 27 ga watan Maris, 2016 a dakin taro […]

Marubutan Hausa sun nemi a tashi tsaye wajen tallafa wa harshen
Marubutan Hausa sun nemi a tashi tsaye wajen tallafa wa harshen

Gabatarwa:
Gamayyar kungiyoyin marubuta kagaggun labarai na fadin Najeriya da sauran kasashen da suke amfani da Hausa a fadin Afirika ta Yamma,   sun gudanar da Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya wanda shi ne irinsa na farko.
An yi wannan taro ne daga ranar Asabar 26 zuwa Lahadi 27 ga watan Maris, 2016 a dakin taro na Mambayya, Gwammaja, Kano daga karfe 10 na safe zuwa 5 na yamma.
Taron ya samu halartar masana daga jami’o’i da Mudaba’anta da ’yan kasuwa da kafafen yada labarai na gida Najeriya da kasashen waje. An samu mahalarta taron da ba su gaza 650 ba a kowace rana. An gabatar da Makalu guda biyar, ta farko wacce ita ce bakandamiya ita ce mai taken: Rubutun Adabi Jiya da Yau: kalubale da Madosa sauran makalun sun hada da Muhimmancin Bincike a Lokacin Rubutu da Dabarun Rubuta kagaggun Labarai da ka’idojin Rubutu da Daidaitacciyar Hausa da kuma Hanyoyin Tallata Ayyukan Marubuta a Kafar Yanar Gizo.     
Abin Lura:
Wannan taro ya binciko abubuwa da suke bukatar canji, wadannan abubuwa su ne kamar haka:
1-A garuruwan Hausawa a yau ba a kai yara makaranta sai inda ba za su yi magana da harshen Hausa ba. 2-Akwai bukatar gwamnatocin Arewa su sauya ga yadda suke riko ga irin wadannan tarurruka na ciyar da Harshen Hausa gaba. 3-Gwamnati ba ta amfani da marubuta kagaggun labarai wajen wayar da kai a kan abubuwan da suka shafi al’umma.
Sauran al’amuran sun hada da: 3-Akwai karancin amfani da littattafan Hausa a cikin manhajar karatu, musamman a Arewacin kasar nan. 4-Marubuta suna bukatar tallafin gwamnati ta wurare da dama. 5-Al’amurran adabin Hausa sun yi karanci a cikin internet. 6-Akwai jami’o’i a jihohi da kasashen da ake Hausa amma ba a koyar da Hausa a cikinsu.
Shawarwari:
Kasancewar wadannan abubuwa da aka ambata a sama, wannan taro ya samar da shawarar cewa akwai bukatar:
Jama’a da gwamnati su rika yi wa yara amfani da Hausa a cikin koyar da su karatunsu kamar yadda ake yi a tsarin ilimi da ya gabata lokacin Turawa, domin yin hakan ba zai kawo tawaya a karatun yaran ba.
Gwamnati ta samar da kasafi kudi ta yadda za a ware kudi don irin wadannan ayyuka na raya harshe da adabi. Kasancewar kowane ci gaba na al’umma ba ya samuwa sai an danganta shi da harshe.
Gwamnati ta dinga amfani da marubuta kagaggun labarai wajen wayar da kai a kan abubuwa da suka shafi al’umma kamar, shaye-shaye da dangoginsa.
Akwai bukatar shigar da wadannan littatafai na kagaggun labarai cikin manhajar koyarwa a makarantun yaranmu.
Gwamnati ta yi hobbasa wajen tallafa wa marubuta, wanda hakan tallafa wa rubutu ne.
Akwai bukatar majalisar dokoki ta jihohi su samar da dokokin da za su tallafa wa rubutu da marubuta.
Akwai bukatar samar da ayyukan adabin Hausa a internet.
Dukkanin jami’o’in da suke jihohi da kasashen Hausa, su rinka koyar da Hausa.