Marwa ya ba PDP Naira miliyan uku don tarbar Shugaban kasa

Tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa, a karkashin Jam’iyyar CPC da ya koma PDP kwanakin baya, Janar Muhammadu Buba Marwa ya ba Jam’iyyar PDP Naira miliyan uku a matsayin gudumuwa don tarbar Shugaban kasa Goodluck Jonathan da zai ziyarci jihar.Janar Marwa ya ce yana da kyakkyawar fata game da shugabannin PDP a jihar, cewa za […]

Marwa ya ba PDP Naira miliyan uku don tarbar Shugaban kasa
Marwa ya ba PDP Naira miliyan uku don tarbar Shugaban kasa

Tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa, a karkashin Jam’iyyar CPC da ya koma PDP kwanakin baya, Janar Muhammadu Buba Marwa ya ba Jam’iyyar PDP Naira miliyan uku a matsayin gudumuwa don tarbar Shugaban kasa Goodluck Jonathan da zai ziyarci jihar.
Janar Marwa ya ce yana da kyakkyawar fata game da shugabannin PDP a jihar, cewa za su gudanar da adalci ga daukacin ’ya’yan jam’iyyar.
Ya kara da cewa zai ci gaba da taimakawa da ba jam’iyyar goyon baya don ganin ta kai ga lashe daukacin zabubbukan da za a gudanar a badi, domin haka ya nemi jama’ar Adamawa su ci gaba da mara wa PDP baya.
Ya ce an dakatar da zuwan Shugaban kasa jihar ne bisa dalilan tsaro musamman sace ’yan mata ’yan makarantar 276 da ’yan bindiga suka yi a Chibok da ke Jihar Borno. Ya ce kada hakan Ya damu mambobin Jam’iyyar PDP.
Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Adamawa Cif Joel Madaki ya bayyana jin dadinsa game da shigowar Janar Marwa cikin jam’iyyar, wanda ya ce dama suna tsammanin shigowarsa.
Mista Joel Madaki ya tabbatar da cewa jam’iyyar za ta gudanar da adalci ga daukacin mambobinta. Ya ce duk mai bukatar tsayawa takarar wani mukami a PDP, kofa bude take muddin jama’arsa suna sonsa.
A wani labarin Jam’iyyar PDP ta shirya wa tsohon Shugaban Jam’iyyar ta kasa, Alhaji Bamanga Tukur liyafar karramawa a jihar inda aka gabatar da jawabai da dama a yayin taron, suka aka jinjina wa Bamanga a matsayin gwarzon dan PDP.
A jawabin Alhaji Bamanga Tukur, ya ce burinsa ya cika domin ya dora PDP a bisa turbar da za a dama da ita. Ya ce bai yi nadamar yadda ya gudanar da sha’anin shugabancin PDP a Najeriya ba.