Mary J. za ta yi waka a bikin Kim da Kanye West
Fitaccen mawakin nan, Kanye West ya zabi zabiya Mary J. Blige ta kasance wacce za ta taya shi nishadantar da mahalarta bikin aurensa da Kim Kardashian.Shi dai mawakin, ya kasance daya daga cikin masoya zabiya Mary, wacce ta dade a cikin sana’ar waka, musamman ma ta yi suna da fitattar wakarta mai taken Eberything. Bikin […]

Fitaccen mawakin nan, Kanye West ya zabi zabiya Mary J. Blige ta kasance wacce za ta taya shi nishadantar da mahalarta bikin aurensa da Kim Kardashian.
Shi dai mawakin, ya kasance daya daga cikin masoya zabiya Mary, wacce ta dade a cikin sana’ar waka, musamman ma ta yi suna da fitattar wakarta mai taken Eberything.
Bikin auren nasu dai, ana sa ran za a gudanar da shi ne a ranar 24 ga watan jibi, amma tun yanzu ma’auratan da abokansu suke ta shirye-shirye, inji kafar watsa labaran ’yan fim din Amurka ta intanet, HollywoodLife.com
Kamar yadda Aminiya ta kalato, ma’auratan, Kanye da Kim, sun amince da cewa Mary ce mawakiya ta farko da suka zaba ta yi wasa a bikin nasu, musamman ma saboda sun dade da kasancewa masu kaunar wakokinta. Don haka suka yanke kudurin ba ta dama ta barje guminta, sannan ta samar da babban tarihi ga bikin auren nasu.
Kanye dai a bana ya cika shekara 36 a duniya, a yayin da amaryarsa Kim ta cika shekara 33. Babu shakka sun kuduri aniyar shirya gagarumin bikin auren da babu irinsa a duniyar makada da mawakan Amurka, kamar yadda wata majiya ta bayyana.