Maryam Lawan Gwadabe: Yada ilimin Fasahar Sadarwa tun daga tushe
Ba ta da burin da ya wuce ganin na kasa da ita sun tasa, musamman a fannin fasahohin zamani.
A wani abu da za a iya cewa ba kasafai ake samu ba tsakanin ’ya’ya mata, musamman a Arewacin Najeriya, Maryam Lawan Gwadabe ta yi zarra wajen ilimin na’ura mai kwakwalwa da na fasahar sadarwa (ICT).
Kwararriyar mai bincike ce, gogaggiyar ’yar kasuwa, mai zane-zane kuma fitacciyar mai ilimin tallace-tallace ta intanet.
- Tauraruwar Arewa: Watan girmama matan Arewa ya tsaya
- Laylah Ali Othman: Matashiyar da ba ta san zaman banza ba
Tauraruwar tamu ta yau ba wai kawai burinta a rika faden sunanta ba ne, tana kuma kwadayin ganin ta inganta rayuwar na kasa da ita, ta yadda su ma za su shahara ta sanadiyyarta, musamman a fannin fasahohin zamani.
Hakan ne ma ya sa ta assasa cibiyar kirkire-kirkire mai suna Blue Sapphire Hub, don ganin tana horar da mutane a bangarorin da ta yi zarra a kansu.
Burinta shi ne ganin ta karfafa wa mutane gwiwa, ba tare da la’akari da shekarunsu, yankin da suka fito ko jinsin su ba, wajen ganin an dama da su a fannin fasahar sadarwa, ta yadda boyayyar baiwar da suke da ita za ta fito, har su ci gajiyar ta.
Ban da Blue Sapphire, Maryam Gwadabe ta kuma kirkiro shirye-shirye da dama da za su tallafa wa mata da matasa a bangaren fasaha domin su dogara da kawunansu.
‘Daya daga cikin fitattun matasa a Afirka’
La’akari da irin tarin gudunmawar da take bayarwa a al’umma, jaridar Forbes ta ayyana sunan Tauraruwar tamu a matsayin daya daga cikin matasa 30, ’yan kasa da shekara 30 da suka yi rawar gani a shekarar 2020.
Wani karin abin sha’awa game da Tauraruwar tamu shi ne a yayin taron ERBSS da aka gudanar a Dubai a 2015, makalar da ta gabatar ce aka ayyana a matsayin wacce ta fi ta kowa a bangaren fasahar sadarwa.
Bugu da kari, a shekarar 2021, tana daya daga cikin mutanen da suka halarci taron kimiyya da fasaha na IVLP da Shahen Harkokin Wajen Amurka ya shirya.
Ta yi digirinta na farko a fannin Injiniyancin Na’ura Mai Kwakwalwa (Software Engineering) daga Jami’ar Coventry, da kuma digiri na biyu a fannin Gudanawar Na’ura Mai Kwakwalwa daga Jami’ar Middlesex da ke Birtaniya.