Maryam Magarya: Mahaifiyata ta raka ni na shiga fim

Maryam Bello Usman wadda aka fi sani da Maryam Magarya na daya daga cikin jarumai mata masu tasowa a masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood, a hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara fim, matsalolin da ta fuskanta da kuma nasarorin da ta cimma. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Tarihina a […]

Maryam Magarya: Mahaifiyata ta raka ni na shiga fim
Maryam Magarya: Mahaifiyata ta raka ni na shiga fim

Maryam Bello Usman wadda aka fi sani da Maryam Magarya na daya daga cikin jarumai mata masu tasowa a masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood, a hirarta da Aminiya ta bayyana yadda ta fara fim, matsalolin da ta fuskanta da kuma nasarorin da ta cimma. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Tarihina a takaice:
Sunana Maryam Usman, kamar yadda ya zama a al’ada a masana’antar fina-finan Hausa, yawanci jarumai mata sukan samu lakabi ko da daga fim din jarumar na farko, ko kuma a rika yi mata lakabi da sunan kamfanin da take, don haka lokacin da na shiga harkar fim sai na kasance a karkashin kamfanin Magarya Production, dalilin da ya sa ake yi mini lakabin ‘Maryam Magarya’ ke nan. A yanzu shekarata 19, an kuma haife ni a Kawo da ke karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano, amma na girma a barikin ’yan sanda da ke Bompai.
Bayan makarantar firamare na fara karatu a Sakandaren Gwamnati ta ’Yan mata a Albasu, Jihar Kano, daga bisani na kammala a Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Kano.
Rayuwata ina karama abar sha’awa ce, an koya mini yadda zan girmama na gaba da ni, an koya mini in rika hakuri da abin da nake da shi, ban taba tunanin zan zama jaruma ba duk da kasancewar ina kallon fina-finan Hausa sosai, ni irin mutanen nan ne da suke matukar sha’awar kallon fina-finai. A lokacin da nake karama ba na iya tantance irin fim din da zan kalla, duk inda na ga ana kallo zan tsaya in kalla. Ina tsammani kallon fina-finai da nake yi ma sun taka rawa har na zama jaruma.
Yadda na zama jaruma
Kamar yadda na fada muku tun a farko, ba ni da burin zama jaruma, to bayan na kammala sakandare sai Allah Ya hada ni kawance da wata, ita wannan kawar tawa jaruma ce, to a lokacin nakan raka ta wuraren da ake daukar fim, sannu-a-hankali na fara sha’awar harkar fim. Duk da haka wannan bai sa na kagu don in zama jaruma ba, sai da aka zo gwajin wani rol kafin a dauke shi ne, sai aka nemi in gwada shi, bayan na gwada ne sai daraktan fim din ya ce akwai yiwuwar in zan zama fitacciyar jaruma idan har zan yi aktin. Daga nan ya ce me ya sa ba zan gwada aktin ba?
Maganganunsa sun dade suna yawo a zuciyata, daga baya na fara tunanin in zama jaruma, na yanke shawarar ne bayan na fada wa kaina cewa, idan har darakta zai ce mini zan iya zama fitacciyar jaruma, to ban ga da dalilin da zan bari wannan baiwar ta tafi a banza ba. Daga nan na sanar wa mahaifiyata cewa zan shiga harkar fina-finan Hausa, mahaifiyata ta yi mini nasiha a kan in guji duk abin da bai dace ba a harkar, in tsare mutuncina, sannan da mahaifiyata muke je wurin kamfanin da ya yi mini rijista, ita ce kuma ta sanya hannu a takardar amincewar in fara harkar fim.
A takaice na shiga harkar fim ne ta hanyar da ta dace, kuma ina alfahari da hakan, tun daga wannan lokacin na rika samun fina-finai kamar ruwan sama, ina alfahari da kasancewata jaruma duk da cewa ina da wadansu burin da nake so in cimma, musamman ta bangaren karatu.
kalubale daga ’yan uwa
Duk da cewa da amincewar mahaifiyata na shiga harkar fim, na fuskanci kalubale daga ’yan uwana, dalilin kalubalen kuwa shi ne, sun yi wa masana’antar fina-finan Hausa mummunar fahimtar, ga wadanda ba su san harkar fim ba, suna yi wa ’yan fim bahagon kallo, suna yi wa masu harkar kallo mutanen banza ko kuma wadanda aka kore su a makaranta. A kowace sana’a a duniya, akwai nagari da kuma bata-gari, amma hakan ba zai sa a ajiye kowa a rukuni daya ba. Na yi iya bakin kokarina wajen yi musu gamsasshen bayani, inda na ci sa’a suka fahimci dalilaina, a yanzu haka suna yaba mini a kan rol din da na taka a wani fim.
kalubalen da na fuskanta
A karo na farko, na fuskanci kalubale a matsayina ta wadda ta samu kanta cikin sabon al’amari, sannan ga karancin shekaru saboda a kwanakin nan ne na cika shekara 19. Na fuskanci matsalar mu’amala da abokan harkarta musamman ma wadanda suka jima a harkar fim, duk da cewa suna daraja ni da kuma martaba ni. kalubale na biyu shi ne yadda a wani lokaci ake neman tauye mutum duk a dalilin kishi ko hassada, a matsayinka na dan Adam dole za ka rika tsoron masu hassada da kuma kishi. Na fuskanci irin wadannan matsalolin, amma na gode Allah komai ya wuce.
Nasarori
A cikin kankanen lokaci na samu nasarar yin manyan fina-finai masu dogon lokaci da ke nunawa a gidan talabijin, wato wanda ake kira Tb Series, na kuma yi manyan fina-finai sama da 7. Ni na jagoranci fim din Ibro na karshe mai suna ‘Babban Direba’. A yanzu haka ni ce babbar jaruma a wani fim mai suna ‘Sarki Abdullah’, inda a yanzu haka kowa maganar fim din yake a industiri.
Burina a bangare karatu
Kowa ya san ilimi jigo ne rayuwar dan Adam, a yanzu haka ina yunkurin fadada karatuna a wata makarantar gaba da sakandare a nan Kano. Na riga na shirya yadda zan hada fitowa a fim da kuma karatu, kasancewar dukkansu suna da muhimmanci a rayuwata. Abin da yake kara karfafa mini gwiwa in koma makaranta ke nan.
Batun aure
A yanzu dai babu batun aure, amma idan ya zo ba zan wuce lokaci ba, shi ya sa ake cewa matar mutum kabarinsa.