Masallaci mai shekara dubu ya bude kofarsa ga mata a Indiya

A karon farko masalalci mai shekara dubu da ke Thazhathangady a garin Kottayam a yankin Kerala ta kasar Indiya ya bude kofarsa ga  mata Musulmi.An kyale su shiga, su gano irin kawa da zayyana mai tsohon tarihi da ke cikin masallacin.Dubban Musulmin mata, wadanda suka hada da ’yan yawon shakatawa, wadanda suka fito daga Kerala […]

Masallaci mai shekara dubu ya bude kofarsa ga mata a Indiya
Masallaci mai shekara dubu ya bude kofarsa ga mata a Indiya

A karon farko masalalci mai shekara dubu da ke Thazhathangady a garin Kottayam a yankin Kerala ta kasar Indiya ya bude kofarsa ga  mata Musulmi.
An kyale su shiga, su gano irin kawa da zayyana mai tsohon tarihi da ke cikin masallacin.
Dubban Musulmin mata, wadanda suka hada da ’yan yawon shakatawa, wadanda suka fito daga Kerala da kasashen waje sukan cika masallacin. An bayar da damar ne saboda bukatar kyale mata su shiga wuraren ibada da ta samu karbuwa.
“Wannan masallaci ne mai shekara dubu. Matan mu na bukatar son ganin sa, kuma suna da bukatar ziyarar wurin ibada mai tsarki. Don haka kwamitin masallacin ya yanke matsaya wajen bai wa mata dama su ziyarci wannan wuri tun daga ranar 24 ga Afrilu zuwa 8 ga Mayu,” a cewar Nawab Mulladom, Shugaban Kwamitin kula da Masallacin.
Ba a bude masallacin saboda ‘kowane irin biki ko salloli. Ana bude shi ne kawai don mata su gane wa idanunsu yadda wurin yake,” a cewarsa, inda ya kara da cewa, a kan umarci maza su fice daga masallacin kafin matan su shigo. Matan Musulmi kan sanya tufafin al’ada kafin su kai ziyara wurin.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano