Masallacin Annabi da ke Madinah

Babi na Shida: Wanda bai daukar wasi-wasi da makamancinsa a cikin rikitattun al’amura: 511. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “dan Uyainatu ya ba mu labari daga Zuhuri daga Abbad dan Tamim daga Baffarsa ya ce, “An kai kuka ga Annabi (SAW) game da mutumin da yake jin (samun) wani abu cikin ransa kamar […]

Masallacin Annabi da ke Madinah
Masallacin Annabi da ke Madinah

Babi na Shida: Wanda bai daukar wasi-wasi da makamancinsa a cikin rikitattun al’amura:

511. An karbo daga Abu Nu’aim ya ce: “dan Uyainatu ya ba mu labari daga Zuhuri daga Abbad dan Tamim daga Baffarsa ya ce, “An kai kuka ga Annabi (SAW) game da mutumin da yake jin (samun) wani abu cikin ransa kamar ya yi tusa a Sallah shin zai yanke Sallar? Ya ce, “A’a, sai ya ji sauti ko wari.” dan Abu Hafsa ya ce, daga Zuhuri cewa: “Babu sake alwala sai ga wanda ya ji warin tusa ko ya ji sauti.”
512. An karbo daga Ahmad dan Middam Al-Ajali ya ce: “Muhammad dan Abdurrahman dufa’iyyu ya ce, “Hisham dan Urwata ya ba mu labari daga Babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), cewa: “Lallai wasu mutane sun ce, “Ya Manzon Allah! Lallai wasu mutane suna zuwa mana da nama, ba mu sanin ko sun ambaci sunan Allah a kansa ko a’a.” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ku ambaci sunan Allah, ku ci.”

Babi na Bakwai: Da fadar Allah Madaukaki cewa, “Idan suka ga kayan fatauci ko wani abin shagala sai su watse zuwa gare shi…” (k:62:11):
513. An karbo daga dalku dan Ghannam ya ce: “Za’idatu ya ba mu labari daga Husain daga Salim ya ce, “Jabir (Allah Ya yarda da shi) ya ba ni labari, ya ce, “Wata rana muna Sallah tare da Annabi (SAW), sai wasu jama’a daga Siriya (Sham) suka gabato suna dauke da kayan fatauci na abinci. Sai wasu suka waiwaya gare su, suka watse har ya rage babu wanda ya saura tare da Annabi (SAW) face mutum goma sha biyu, sai wannan aya ta sauka cewa: “Idan suka ga kayan fatauci ko wani abin shagala sai su watse zuwa gare su…” (k:62:11).

Babi na Takwas: Wanda bai kula da wurin da ke samun dukiya:
514. An karbo daga Adamu ya ce: “dan Abu Zi’ib ya ba mu labari ya ce, Sa’idul Makburi ya ba mu labari daga Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi) daga Annabi (SAW) ya ce, “Wani zamani zai zo ga mutane mutum bai kula (kiyayewa) daga abin da yake samu (karba) shin daga halal ne, ko daga haram ne?”

Babi na Tara:
Kasuwanci a game da tufafi da wasu abubuwa. Bisa fadar Allah Madaukaki cewa: “Wasu mazaje kasuwanci da fatauci ba sa shagaltar da su game da ambaton Allah…” (k:24:37). kattada ya ce, “Mutane sun kasance suna kasuwanci (saye da sayarwa), kuma suna jaura amma su idan wani abu daga hakki daga hakkokin Allah Ya gabato kasuwancinsu ko fataucinsu ba ya shagaltar da su game da ambaton Allah har sai sun bayar da shi yadda Allah Yake so:

 515. An karbo daga Abu Asim ya ce: “Daga Juraij ya ce, Amru dan Dinar ya ba ni labari daga Abu Minhal ya ce: “Na kasance ina jaura (kasuwanci) ta hanyar musanya (canjin kudade), sai na tambayi Zaidu dan Arkam (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Annabi (SAW) ya fadi haka ne-Hawwala Sanad- ya ce, “Fadalu dan Yakub ya ba ni labari, ya ce, Hajjaju dan Muhammad ya ba ni labari ya ce, dan Juraij ya ba mu labari ya ce, Amru dan Dinar ya ba ni labari da Amir dan Mus’ab cewa, “Lallai su sun ji Abu Minhal yana cewa: “Na tambayi Barra’u dan Azib da Zaid dan Arkam game da cinikin musanyar kudade sai suka ce, “Mun kasance attajirai a zamanin Manzon Allah (SAW) sai muka tambayi Manzon Allah (SAW) game da cinikin musanyar kudade sai ya ce, “Idan ya kasance hannu da hannu to babu laifi, amma idan ya kasance da jinkiri ba ya halatta.”