Masallacin da aka shekara 60 ba a fuskantar alkibla daidai

Majalisar Limamai da Malamai ta daidaita alkiblar masallacin da aka yi kuskure kanta shekara 60

Masallacin da aka shekara 60 ba a fuskantar alkibla daidai

Yadda ‘yan dubban mutane kalilan suka gudanar da Aikin Hajji a bara. Reuters

Wasu Musulmi da suka kaurace wa yin Sallah a Babban Masallacin garin Iseyin a Jihar Oyo a dalilin zargin karkatar da alkiblar masallacin sun yi na’am da aikin daidaita tsayuwar alkiblar masallacin da Majalisar Limamai da Malamai na garin Iseyin ta gudanar a makon jiya.

Majalisar ta tabbatar da cewa, an yi kuskuren tsayar da tsohuwar alkiblar ce shekara 60 da suka gabata.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce Limamin Babban Masallacin da ke Unguwar Oja-Oba a garin Iseyin, Sheikh Abdul-Hakeem Babatunde Olajori, ya jagoranci dubban Musulmi wajen yin sallar Juma’a da sabuwar alkiblar da aka daidaita tsayuwarta.

An gudanar da Sallar ce tare da jama’ar Musulmin da suka kaurace wa yin Sallah a masallacin saboda matsalar karkacewar alkiblarsa.

Babban Limamin ya yi wa ’yan jarida karin bayani a kan wannan muhimmin aiki da majalisar ta gudanar na daidaita alkiblar masallacin.

Ya ce, majalisar ta sauya wa kabarin marigayi tsohon limamin masallacin, Imam Alalukimba wani wuri da ya fi dacewa fiye da wajen da aka gina kabarin a Gabas da tsohuwar alkiblar masallacin.

An canza matsugunin kabarin ne ta hanyar tone kabarin da gina sabon kabarin da amincewar zuri’ar tsohon limamin, domin Manzon Allah (SAW) ya hana yin Sallah a inda ake fuskantar kabari ko makabarta.

“Wadannan abubuwa biyu da suka hada da aikin daidaita alkiblar masallacin da sauya kabarin tsohon limamin suna da muhimmanci sosai don aiki ne da umarnin Annabi (SAW) da ya zama alama ce ta rahamar Ubangiji ga al’ummar Iseyin da Jihar Oyo da kasa baki daya,” inji Babatunde Olajori.

Binciken Aminiya ya gano cewa, akwai wasu manya da kananan masallatai a garuruwan jihohihin Kudu maso Yamma wadanda tuni majalisar ta kammala aikin daidaita tsayuwar alkiblarsu.

Ana aikin sauya alkiblar wadannan masallatai ne ta hanyar sanya (sitra) da karkatar da shimfidar liman a yayin da ake rusa katangar wasu masallatan domin gina sabuwa da ta yi daidai da fuskantar Dakin Allah.