Masana kimiyya a Amurka sun gano sabbin duniyoyi 8
A shekaranjiya Laraba ne masana ilimin taurari a kasar Amurka sun gano wasu sababbin duniyoyi takwas da suke da halittu masu kaman da na duniyar da muke rayuwa a cikinta wato Earth. Masanan sun hango duniyoyin ne ta yin amfani da na’urar hango halittun sararin samaniya, bayan kwashe shekaru 20 suna bincike a kansu. Masu […]
A shekaranjiya Laraba ne masana ilimin taurari a kasar Amurka sun gano wasu sababbin duniyoyi takwas da suke da halittu masu kaman da na duniyar da muke rayuwa a cikinta wato Earth.
Masanan sun hango duniyoyin ne ta yin amfani da na’urar hango halittun sararin samaniya, bayan kwashe shekaru 20 suna bincike a kansu. Masu binciken sun ce akwai yiwuwar a samu duwatsu da tekuna a cikin sababbin duniyoyin kamar yadda duniyar Earth take da su, sannan kuma suma suna da wasu hallittun da za su iya taimaka wa mutum ya rayu.
Sabbin duniyoyin kanana ne, domin duniyar Earth ta rubanyasu sau biyu a girma, sannan kuma ba su da matsanancin yanayin zafi ko sanyi. Kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito.
Sai dai masanan ba su fadi ko akwai wata daga cikin duniyoyin takwas ba da dan Adam zai iya rayuwa a cikinta ba, sai dai sun nuna hakan abu ne da zai iya yiwuwa. Sun ce babu wani bil’adama da zai iya zuwa inda duniyan guda 8 suke nan da wani lokaci mai tsawo, domin suna da nisan daruruwan shekaru daga inda haske yake.