Masana kimiyya sun samar da lantarki daga fitsari
Masana kimiyya sun samar da dabarar sarrafa kananan kwayoyin halitta don samar da makamashin wutar lantarki daga fitsari. Wannan sabuwar fasahar kimiyya, za ta kawo sauyi a harkar samar da makamashi, inda gungun masu bincike daga Jami’ar Bath da ta kueen Mary da ke Landan da dakin bincike na Bristol Robotics Laboratory suka gudanar.“Man da […]
Masana kimiyya sun samar da dabarar sarrafa kananan kwayoyin halitta don samar da makamashin wutar lantarki daga fitsari. Wannan sabuwar fasahar kimiyya, za ta kawo sauyi a harkar samar da makamashi, inda gungun masu bincike daga Jami’ar Bath da ta kueen Mary da ke Landan da dakin bincike na Bristol Robotics Laboratory suka gudanar.
“Man da aka samar daga kananan kwayoyin halitta na dibge da dimbin makamashin halittu da ake samarwa daga gurbatattun abubuwa da ake fitarwa daga jiki da suka hada da fitsari,” a cewar Mirella Di Lorenzo, daya daga cikin marubutan hadin kwiwa a binciken da ya fito daga Jami’ar Bath.
“A duniya ana zubar da dimbin fitsari, don haka idan muka yi amfani da wannan dama ta gurbatattun abubuwan da ake zubarwa, tare da tatsar man da ke bubbugowa daga kananan kwayoyin halitta, za a kawo sauyi wajen samar da lantarki,” inji Lorenzo.
Wannan sabuwar dabharar tatso man kananan kwayoyin halitta, an yi bayaninta a cikin mujallar kimiyyar makamashin lantarki ta “Electrochimica Acta,” inda aka bijiro da cewa ba a bukatar kayan aiki masu tsada na hada turken zukar sinadaran lantarki na “cathode,” wamnda ake kera shi da sinadarin Carbon da wayar Titanium. Don samun lantarki cikin sauki, sinadaran kan yiwo taho-mu-gama, inda akan yi amfani da sinadaran glucose da obalbumin da ake samun su a farin tantanin da ke lullube da gwaiduwar kwai.
“Man da ake zukowa daga kananan kwayoyin halitta zai iya zama babban jigo wajen samar da makamashi a kasashe masu tasowa, musamman masu fama da talauci da yankunan karkara,” a cewar Jon Chouler, shugaban marubutan binciken.
“Sabon tsarin na da arha, sannan ga shi da inganci fiye da tsare-tsaren al’ada daka saba da su.Kayan aiki irin wadannan za su samar da wutar lantarki daga fitsari, da za su bayar da sabuwar dabarar samar da makamashi mai dorewa, daga gurbatattun abubuwa,” inji Chouler.