Masana sun fara bincike kan yadda mata tsofaffi za su iya daukar ciki

Binciken zai ba matan da suka manyanta damar daukar ciki da haihuwa

Masana sun fara bincike kan yadda mata tsofaffi za su iya daukar ciki

Wata mace mai juna biyu (Tsohuwar ajiya)

Wasu kwararrun likitoci a Amurka na kokarin amfani da kimiyya wajen rage saurin tsufan mahaifa, domin ba wa mata tsofaffi damar daukar ciki. 

Mataimakiyar Farfesa a bangaren binciken tsufa da ke jami’ar Buck a jihar Califonia, Jennifer Garrison ce ta bayyana hakan, ta cikin wani shiri da gidan talabijin na CNN, inda ta ce binciken ya kuma gano cewa matan da suka daina haihuwa daga shekara 40, na cikin hatsarin mutuwa da wuri da fiye da kaso 40.

Haka kuma ta ce duk da cewa da zarar mace ta kai shekarun haihuwa 30 ko gab da haka, dukkan  jikinta kan yi aiki fiye da ko yasuhe, in banda mahaifarta.

Garrison ta ce hakan na faruwa ne saboda a wannan lokacin ta fara nuna alamun tsufa.

A cewarta, matsalar ba a iya nan ta tsaya ba, domin da zarar mahaifar ta daina sakin sinadaran da ke sanya daukar ciki, tana hadawa har da wasu da ke taimakawa ingancin lafiyar jiki baki daya.

Haka kuma ta ce matsalar tsufan mahaifa ko ga lafiyayyar mace, na kara hatsarin kamuwa da ciwon zuciya da rashin bacci da mantuwa da kiba da sauran larurorin tsufa..

Sai dai ta ce da wannan kimiyya duk wadannan matsaloli za su zamo tarihi.

Harin Borno: Mun kashe ’yan ta’adda 34, mun rasa dakaru 6 – Sojoji

Radda ya yi wa Kwamishinoni sauyin ma’aikatu a Katsina

G-Fresh da Babiana sun nemi a saki Baɗejo

DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani suka shafe na Hausawa