Masana sun nemi saninsa (1)

A wannan makon za mu yi nazari ne a kan muhimmancin sanin Yesu Almasihu. Kamar yadda muka sani muna cikin watan Kirsimeti, mutane da yawa a fadin duniya na shirin wannan biki.  Da yawa sukan yi tafiya mai nisa don wannan biki, wasu kuma kan yi sayayya don ba da kyauta. Hakan Kirsimeti lokaci ne […]

Masana sun nemi saninsa (1)
Masana sun nemi saninsa (1)

A wannan makon za mu yi nazari ne a kan muhimmancin sanin Yesu Almasihu. Kamar yadda muka sani muna cikin watan Kirsimeti, mutane da yawa a fadin duniya na shirin wannan biki.  Da yawa sukan yi tafiya mai nisa don wannan biki, wasu kuma kan yi sayayya don ba da kyauta. Hakan Kirsimeti lokaci ne na nuna kauna kamar yadda muka sani a littafin Yahaya 3:16; “Saboda kaunar da Allah Ya yi wa duniya har ya ba da makadaicin dansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya samu rai madauwami”.    Lokaci ne na farin ciki, Luka 2:8-11. A wannan yankin kasa kuwa da yawan makiyaya suna kwana a fili, suna tsaron garken tumakinsu da daddare. Sai ga wani mala’ikan Ubangiji a tsaye kusa da su, daukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, har suka tsorata gaya, Sai mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ga shi, albishir na kawo muku na farin ciki mai yawa, wanda zai zama na dukan mutane. Domin yau an haifa muku mai ceto a birnin Dawuda, wanda yake shi ne Almasihu, Ubangiji.
Wani abin da za mu duba a wannan karo shi ne muhimmancin sanin Yesu Almasihu.        
Bari mu duba cikin littafin Matta 2:1-12; Sa’ad da aka haifi Yesu a Baitalami na kasar Yahudiya, a zamanin Sarki Hirudus, sai ga wadansu masana taurari daga gabas suka zo Urushalima, suna cewa, “Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.” Da Sarki Hirudus ya ji haka, sai ya damu kwarai, haka kuma dukkan mutanen Urushalima. Sai ya tara dukkan manyan firistoci da malaman Attaura na jama’a, ya tambaye su inda za a haifi Almasihu. Sai suka ce masa, “A Baitalami ne, na kasar Yahudiyya, domin haka annabin ya rubuta cewa, ‘Ke ma Baitalami, ta kasar Yahuza, Ko kusa ba ke ce mafi kankanta a cikin manyan garuruwan Yahuza ba, domin daga cikinki za a haifi wani mai mulki, wanda zai zama makiyayin jama’ata, Isra’ila.’
Sai Hirudus ya kira masanan nan a asirce, ya tabbata daga bakinsu ainihin lokacin da tauraron nan ya bayyana. Sannan ya aike su Baitalami, ya ce, “Ku je ku binciko mini wannan yaron nan sosai. In kun same shi, ku kawo mini labari, don ni ma in je in yi masa sujada.” Su kuwa da suka ji maganar Sarki, sai suka yi tafiyarsu. Ga shi kuwa, tauraron da suka gani a gabas yana tafe a gabansu, har ya zo ya tsaya bisa inda wannan yaron yake. Da suka ga tauraron sai suka yi matukar farin ciki. Da suka shiga gidan kuwa, sai suka ga wannan yaro, tare da mahaifiyarsa Maryamu, suka fadi gabansa suka yi masa sujada. Sannan suka kwance kayansu, suka mika masa gaisuwa tare da zinariya da lubban da mur. Amma da aka gargade su a mafarki kada su koma wurin Hirudus, sai suka koma kasarsu ta wata hanya daban.
Idan muka duba a nan masanan nan sun dauki lokacinsu suka yi tafiya mai nisa domin su ga Yesu Almasihu, sun zo da zuciya daya, cike da farin ciki da kauna da kuma kyauta domin su yi masa sujada.
Abin koyi a nan shi ne, masannan nan masu ilimi ne na kwarai, masu arziki ne kuma idan muka ga irin kyautar da suka kawo wa Yesu, “…Sa’an nan suka kwance kayansu, suka mika masa gaisuwa tare da zinariya da lubban da mur.” (Matta 2:11), amma duk da haka sun nemi sannin inda aka haifi Yesu, me ya sa Yesu? Mun san dai a wannan daren ba shi kadai aka haifa ba, an haifi yara da yawa, to, dalili  shi ne haihuwar Yesu Almasihu na da muhimmanci ga dukkan duniya, shi ya sa ya kamata mu nemi saninsa.
Idan muka dubi inda muka karanta a littafin Yahaya 3:16,  sanin Yesu na bukatar ka bada gaskiya gare shi na farko ke nan, dalili shi ne idan muka duba cikin littafin Yahaya 14:6, Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.” Kamar yadda masanan nan suka neme shi da zuciya daya.  Da farko sun ga alama a sararin sama-wani tauraro mai haske ya bayana a sama, daga nan suka gaskanta babu shakka cewa wani abin al’ajibi ya faru a duniya, suka kuma shaida cewa an haifi Sarki …”Ina wanda aka haifa Sarkin Yahudawa? Domin mun ga tauraronsa a gabas, mun kuma zo mu yi masa sujada.” Ba su yi shakka ba suka kama hanya suna bin tauraron domin su samu inda aka haifi Yesu, ba su fasa ba sai da suka same shi, a nan suka yi masa sujada suka kuma ba da kyauta na azurfa da lubban da mur. Da farko sun gaskanta da alamun da suka gani a sararin sama, suka kuma nemi sanin inda aka haife shi har suka samu. Abin koyi a nan shi ne mu gaskanta da abin da Littafi Mai tsarki ya fada, (domin a cikin masu rai a yau ba wanda zai ce ya ga Yesu a lokacin da ya zo duniya) kamar yadda masanan nan suka gaskanta tun ba su ga jaririn da aka haifa ba (suka dauki lokacinsu suka nemi inda yake), sanan mu nemi saninsa ta wurin binciken Littafi Mai tsarki da addu’a, ruhun Ubangiji kuma zai bishe mu, mu kuma gane kamar yadda ya alkawarta mana a cikin littafin  1 Tarihi 28:9 …Idan ka neme shi, za ka same shi, haka kuma a littafin Matta 7:7,8; “Ku yi ta roko, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta kwankwasawa, za a kuwa bude muku. Duk wanda ya roka, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya kwankwasa kuma za a bude masa.
A wannan lokaci na bikin Kirsimeti, ya kamata mu nemi Yesu Almasihu kamar yadda masanan nan suka neme shi da zuciya daya ba tare da shakka ba.  
Da yardar Ubangiji za mu ga hanyoyin da ya kamata mu bi domin sanin Yesu Almasihu mako mai zuwa.