Masana sun soki FIFA kan janye dakatarwar Balogun

UEFA ta bayyana cewa FIFA ba ta da hurumin janye dakatarwar wasa guda da aka sanya wa Balogun.

Masana sun soki FIFA kan janye dakatarwar Balogun

Masana harkar ƙwallon ƙafa da wasu manyan jami’ai sun soki Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA) kan matakin da ta ɗauka na janye dakatarwar wasa guda da aka sanya wa ɗan wasan Amurka, Folarin Balogun, bayan rahotannin da ke cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sa baki a lamarin.

Rahotanni sun ce Balogun ya samu damar buga wasan zagaye na 16 na Gasar Kofin Duniya da Belgium bayan FIFA ta soke dakatarwar da ta biyo bayan jan katin da aka nuna masa.

Masana sun bayyana cewa idan har sa hannun ’yan siyasa ya rinjayi hukuncin FIFA, hakan na iya zama barazana ga ’yancin hukumar wajen gudanar da harkokinta cikin adalci.

Daga cikin waɗanda suka nuna damuwa akwai masanin harkar wasanni Simon Chadwick, da kocin Ingila, Thomas Tuchel, da kuma tsohon shugaban FIFA, Sepp Blatter.

Sun ce irin wannan mataki na iya kafa mummunan misali ga yadda ake tafiyar da harkokin ƙwallon ƙafa a nan gaba.

A baya dai, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Turai UEFA ta bayyana cewa FIFA ba ta da hurumin janye dakatarwar wasa guda da aka sanya wa Balogun.

Kalaman na UEFA sun zo ne bayan shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya sanar da janye dakatarwar Balogun, bayan buƙatar da Shugaba Donald Trump ya gabatar.