Masana’antar fim ta girgiza da rasuwar A’isha dankano

A ranar Talatar da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitacciyar jarumar fim din Hausa da aka fi sani da Kannywood A’isha dankano rasuwa.Duk da cewa marigayiyar ta dan yi jinya na tsawon wata guda kafin rasuwarta amma hakan bai hana abokan sana’arta shiga rudani a daidai lokacin da suka samu labarin rasuwarta ba. […]

Masana’antar fim ta girgiza da rasuwar A’isha dankano
Masana’antar fim ta girgiza da rasuwar A’isha dankano

A ranar Talatar da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitacciyar jarumar fim din Hausa da aka fi sani da Kannywood A’isha dankano rasuwa.
Duk da cewa marigayiyar ta dan yi jinya na tsawon wata guda kafin rasuwarta amma hakan bai hana abokan sana’arta shiga rudani a daidai lokacin da suka samu labarin rasuwarta ba. A cewar mafi yawa daga cikinsu, ba su taba tunanin ciwon nata na ajali ba ne.
Aminiya ta rawaito cewa fitacciyar jarumar ta rasu ne a gidanta da ke unguwar dorayi a yankin karamar Hukumar Gwale, a Jihar Kano; sakamakon fama da ta yi da ciwon kafa na wasu kwanaki, inda a karshe ta ce ga garinku nan.
An haifi marigayiya A’isha a unguwar Gwamamja, yankin karamar Hukumar Dala, Jihar Kano, kimanin shekaru 40 da suka gabata. Ta yi karatunta na firamare har zuwa sakandare a Kano, inda daga nan ta yi aure har ta haifi ’yarta daya. Bayan aurenta ya mutu ne ta shiga harkar fim din Hausa.
Marigayiyar ta shiga harkar fim ne shekaru 19 da suka wuce, inda ta fara fitowa a fim mai suna Bilkisu. Sai dai wani fim da ya fito da ita, shi ne fim din Sima. Haka kuma fim din da ta fito cikinsa na karshe, shi ne fim din kyalkyal Banza, wanda a karshe ma ba ta iya karasa shi ba, sakamkon ciwon da ya yi mata tsanani.
Marigayiyar ta fito a fina-finai masu yawan gaske, haka kuma ta samu kyaututtukan yabo daban-dabn, domin ko a bara ta karbi kyautar MTN/Kannywood Award a matsayin jarumar da ta fi kowa kwarewa a iya shirya mugunta a fim.
Aminiya ta kalato cewa ko a lokacin da marigayiyar take gudanar da sana’arta ta wasan Hausa, a gefe guda kuma ita ma’aikaciyar wuncin gadi ce a gidan Rediyon Jihar Kano, inda take gabatar da wasu shirye-shirye na siyasa da kuma filin yara da sauransu.
Zainab Muhamad Auwal, ita ce tilon diya ga marigayiyar. Ta bayyana cewa duk da cewa rasuwar mahaifiyarta ta doke ta kwarai da gaske, amma ta ji dadin yadda karshen mahaifiyarta tata ya kasance. “Alhamdu lilllahi, mama ta cika da imani domin kalmarta ta karshe ita ce kalmar shahada. A duk lokacin da ciwon kafarta ya motsa, babu abin da za ki ji tana yi sai salati. Wallahi da ta rasu fuskarta a sake kamar tana murmushi. Duk da ina jin ciwon rasuwarta amma idan na tuna hakan nakan ji sanyi a zuciyata.” Inji ta.
Mami dankano kanwa ce ga marigayiyar, ita ce kuma ta yi jinyarta. Ta bayyana wa Aminiya cewa marigayiyar ta dauki tsawon kwanki 30 tana jinya. “Lokacin da ta ji ciwon ya matsa mata sai ta kira ni a waya, ta gaya mini cewa ciwon kafarta fa ya matsa mata. Hakan ya sanya na yi gaugawar zuwa gidanta, inda na same ta da kyar take tashi.
“Dama da yake tana da ciwon jeji, hakan ya sa ciwon kafartata ya yi tsanani, musamman ma lokacin da aka yi mata allura. A nan dai na zauna a gidanta. Kullum idan gari ya waye ciwo sai gaba yake yi har dai Allah Ya yi ikonSa a kanta.” Inji ta.
Maryam Muhamamd makwabciya ce ga marigayiyar. Ta bayyana ta da cewa mutum ce mai hannun kyata, wacce abin duniya bai rufe mata ido ba. “A kullum gidanta cike yake da jama’a, wadanda take taimaka mwa. Babu lokacin da za ka je mata da damuwa ba ta warware maka matsalarka ba kowce iri ce. Ba na mantawa wata makwabciyarmu ta haifi tagwaye, walalhi ita ta yi komai na haihuwar har kayan fitar suna ta yi wa maijegon. A kullum aka yi abinci a gidanta sai ta sa an raba shi fiye da gidaje ashirin a layinmu. Babu abin da za mu yi mata sai dai mu yi addu’ar Allah Ya jikanta.”
’Yan fim da dama sun halarci jana’izarta da suka hada da Rukayya Umar Dawayya da Aina’u Ade da Maryam Tahir da Hauwa Waraka da sauransu. Daga cikin maza kuma akwai irin su Ibrahim Sharukhan da Shugaban Hukuamr Tace Fina-finai ta Jihar Kano, Isma’ila Na’abba Afakallah da Isa A. Isa da Aminu Sheriff Momoh da sauransu.
Rukayya Umar Dawayya ta bayyana marigayiyar da cewa mutum ce mai ibada da son manzon Allah (SAW). Haka kuma babu ruwanta da munafunci ko hassada. “A gaskiya mun yi rashin abokiyar sana’a tagari. Na yi mu’amala da ita sosai, mutum ce wacce babu ruwanta da munafunci ko hassada. Ga ta da ibada da son Manzon Allah (SAW). “ Ta karasa cikin kuka.
Aina’u Ade ta bayyana cewa ta kadu kwarai da gaske da labarin rasuwar marigayiyar, kasancewar ba ta taba tunanin wannan ciwon zai kai abokiyar sana’ar tata lahira ba. “A gaskiya na kadu da rasuwarta, wallahi ban taba tunanin mutuwa za ta yi a wanan lokaci ba. Babu abin da zan ce sai dai mu yi mata addu’a Allah Ya jikanta da rahama, Ya kuma gafarta mata zunubbanta.”
Maryam Tahir ta shaida wa Aminiya cewa sun yi fina-finai masu yawa tare da marigayiyar, wanda hakan ya sa suka shaku sosai. “Muna yawan fitowa a fim tare, hakan ya sa muka shaku, domin ko fim dinta na karshe wanda bai fito ba, wato kyalkyal Banza, tare muka yi shi. A’isha mutum ce da ba ta san munafunci ba, ba ta san kanan maganganu irin na masana’antar fim ba. Idan ka yi mata abu kai tsaye za ta gaya maka kuma shi ke nuna maganar ta wuce har abada.  Ga ta da iya mu’amala. Babau shakka mun yi rashi. Allah Ya ji kanta, Ya yi mata rahama.”
Malam Jamilu Ahmad Yakasai shi ne Shugaban kungiyar ‘Yan fim ta Arewa (AFAN) reshen Jihar Kano. Ya bayyana rasuwar A’isha dankano a matsayin gagarumin rashi ga masana’antar fim, wanda cike gurbinsa zai yi matukar wahala. “A gaskiya mun yi rashi. A’isha dankano ta bayar da gagarumar gudunmaowa wajen ciyar da harkar fim gaba, wanda za a dauki tsawon lokaci ba a cike gurbin da ta bari ba. A’isha mutum ce da ta iya mu’amala da mutane. Idan har ka ji tana fada, to idan ka bincika za ka tarar an taba mutuncinta ko kuma an zalunce ta. Ni zan iya cewa na dade ban ga mutumin da ya iya mu’amala da mutane kamarta ba. Idan ka kira ta aiki ta yi maka ka ba ta hakkinta, to wallahi cikin girmama juna za ku rabu. Babu abin da zan ce sai dai na yi mata addu’ar Allah Ya sa ta huta, Ya kuma yafe mata kura-kurenta. Idan tamu ta zo, Allah Ya sa mu cika da imani.”
Marigayiyar ta rasu ta bar mahaifiyarta da ke zaune a garin Sakkwato da kuma ’yarta budurwa wacce kwanaki goma suka rage a aurar da ita.