Masana’antar haihuwar jarirai ta karbu a Indiya

Talauci ya sanya mata da dama yanke shawarar su rika daukar cikin wadansu mazan domin a biya su kudi a kasar Indiya.Kudin da ake biyan matan da ake yi wa baye domin su dauki cikin wadansu mazan da ba mazajen aurensu ba ya haura dala biliyan daya a Indiya. Kuma a lokacin da suke da […]

Masana’antar haihuwar jarirai ta karbu a Indiya

Matan da aka yi wa baye don daukar cikin wadansu mazanTalauci ya sanya mata da dama yanke shawarar su rika daukar cikin wadansu mazan domin a biya su kudi a kasar Indiya.
Kudin da ake biyan matan da ake yi wa baye domin su dauki cikin wadansu mazan da ba mazajen aurensu ba ya haura dala biliyan daya a Indiya. Kuma a lokacin da suke da juna biyun sukan zauna ne a wani gida da aka bayyana a matsayin masana’antar haihuwar jarirai.
basanti, wata matar aure ce mai shekaru 28 a duniya, kuma tana daga cikin irin wadannan matan, a cewarta “A Indiya iyali na da muhimmanci ta yadda a shirye kake ka yi duk abin da ya kama domin ‘ya’yanka.”
Mijin basanti yana aiki inda yake karbar dala 40 kacal a wata, kuma kudin ba ya isarsu, saboda haka kudin da za ta samu zaitaimaka wajen  sauya rayuwarsu
Ta kara da cewa, “Abin da ya sa na dauki cikin wani shi ne, domin in samu cika burina game da yarana.”
basanti dai tana dauke ne da cikin wadansu ma’aurata ‘yan kasar Japan, kuma za su biya ta dala dubu 8 ne, kudin da zai isa ta gina sabon gida ta kuma tura ‘ya’yanta masu shekaru bakwai da kuma biyar zuwa makarantar da ake koyar da harshen Ingilishi a kasar. Abin da ba ta taba tsammanin za ta iya yi ba, domin haka ta ce, “Ina matukar farin ciki.”
An yi mata bayen ne a birnin Anand na Gujarat, kuma za ta kwashe watanni tara a wani gida da za a dinga kula da ita tare da wadansu mata kamarta su goma.
Dokta Nayna Patel likita ce mai asibitin da ake bayen da kuma gidan da ake kula da matan, ta bayyana cewa, matan ba su da wani iko ko tasiri a rayuwar jariran da za su Haifa. “Ina fuskantar suka game da wannan abin da nake yi mai cike da cece-kuce, akwai zargin da ake mini na cewa wai ina neman kudi ne ta wannan hanyar, wadansu kuma na cewa masana’antar sayar da yara, kuma sukar na da ciwo,” inji Likitar.
A ganinta matan na karbar abin da ya dace, kuma ana koyar da su sana’oin hannu, saboda su samu abin dogaro bayan sun bar gidan.
Dokta Patel tana yarda mace ta dauki ciki har sau uku, kuma yayin goyon cikin ba za su kusanci mazajen aurensu ba, sai dai iyalinsu za su ziyarce su sau daya a mako a yayin da suke zaman goyon ciki.
Ma’auratan da ake haifa wa jarirai kan karbe ‘ya’yan da zarar an haife su, yayin da a wadansu lokutan su kan dauki kwanaki kafin a shirya takardun amincewa a fitar da su daga kasar.
Indiya dai ita ce kasar da ta fi kowace kasa a duniya matan da ke daukar cikin wadansu mazaje ta hanyar baye.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan