Masana’antar Sadarwa ta samar wa Najeriya Naira tiriliyan 1.5 – danbatta
Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC), Farfesa Umar Garba danbatta ya bayyana cewa Masana’antar Sadarwa a Najeriya ta samar da karin Naira tiriliyan 1.549 ga yawan kudin shiga ga Najeriya a cikin watanni shida na farkon shekarar nan. Wannan ya nuna cewa an samu karin kashi 6.88 daga abin da […]

Babban Mataimakin Shugaban Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Najeriya (NCC), Farfesa Umar Garba danbatta ya bayyana cewa Masana’antar Sadarwa a Najeriya ta samar da karin Naira tiriliyan 1.549 ga yawan kudin shiga ga Najeriya a cikin watanni shida na farkon shekarar nan. Wannan ya nuna cewa an samu karin kashi 6.88 daga abin da aka samu a watanni uku na farkon shekara.
A yayin da yake jawabin maraba da Shugabar Hukumar Al’amuran Sadarwa ta kasar Laberiya (LTA), Madam Angelikue Weeks, wacce ta ziyarce shi a makon da ya gabata a Abuja, danbatta ya ce an samu wannan bayanin ne daga rahoton Hukumar kididdiga ta Najeriya (NBS).
Rahoton na hukumar NBS ya nuna cewa an samu karuwar kashi 9.5 na kudaden shiga a watanni uku na biyu, fiye da kashi 9.1 da aka samu a watanni uku na farkon shekarar 2017.
“Muna alfahari da wannan gagarumar nasara da aka samu a wannan fanni na sadarwa, da irin gudunmowar da yake bayarwa, duk kuwa da irin babban kalubalen da ke fuskantar tattalin arzikin kasar nan, amma fannin ya kasance mai kokari da jajircewa.” Kamar yadda shugaban ya fada wa bakuwar tasa, wacce ke tattare da rakiyar shugabannin kungiyar Masu Kula Da Al’amuran Sadarwa Na Afrika Ta Yamma (WATRA).
Haka kuma, Shugaban na NCC ya sake bayyana cewa, an samu karuwar yadda ake amfani da data (tsarin da ke ba mutum damar shiga intanet) a kasar nan. “A duk wata, ana amfani da data ta terabits miliyan 40,” inji shi.
Haka kuma, ya bayyana cewa nan gaba kadan kasar nan za ta bunkasa ta fuskar kimiyyar sadarwa, a lokacin da aka samu karuwar fantsamar data daga Legas zuwa sassan kasar nan, ta hanyar bayar da lasisi ga kamfanoni daban-daban.
Da yake kara bayani dangane da wannan batu, danbatta ya ce ya zuwa yanzu, yawan data da ake samarwa a kasa ya karu zuwa kashi 21 cikin dari, inda ake kokarin tunkarar kashi 30 cikin dari nan da badi, wanda hakan ke cikin burin cin ma wa na samar da faffadar kimiyyar samar da data a kasa.
Ya ce hukumarsu ta amince da gudanar da kasuwanci ta wannan fanni, daga cikin tsarin kudurori 8 na fadada harkokin sadarwa a kasa.