Masar na ƙoƙarin sulhunta ƙazamin rikicin da ake fafatawa a Gaza

Martanin da muke mayar wa Hamas a yanzu somin-taɓi ne —Netanhayahu

Masar na ƙoƙarin sulhunta ƙazamin rikicin da ake fafatawa a Gaza

Gwamnatin Masar na ƙoƙarin yayyafa ruwan sanyi kan wutar ƙazamin rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da mayakan Hamas na Falasdinu tun a karshen makon da muka yi bankwana da shi.

Majiyoyin tsaron Masar biyu sun sanar a ranar Litinin cewa an soma tattaunawa da Isra’ila da Hamas don kokarin dakile barin wuta a tsakaninsu da kuma tabbatar da tsaron Isra’ilawa da mayakan Falasdinawa suka yi garkuwa da su.

Masar ta bukaci Isra’ila da ta yi taka-tsan-tsan, sannan Hamas da ta rike mutanen da ta kama cikin yanayi mai kyau domin a bude yiyuwar sulhu nan ba da jimawa ba, duk da cewa hare-haren da Isra’ila ta kai a jere a zirin Gaza ya sanya sasantawa ta yi wuya, in ji majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu.

Mayakan Falasdinawa sun yi garkuwa da mutane da dama a wani harin da kungiyar Hamas ta kaddamar daga Zirin Gaza a ranar Asabar, wanda ya hada da sojoji da fararen hula, yara da kuma tsofaffi.

Wata kungiyar gwagwarmaya ta Falasdinu mai suna Islamic Jihad ta ce tana rike da sama da 30 na wadanda aka kama.

Jiragen yakin Isra’ila da jirage masu saukar ungulu da makaman atilare sun yi ta luguden wuta a zirin Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke fafatawa don fatattakar mayakan Falasdinawa da suka tsallaka daga Gaza.

Yankin Sina’i na Masar yana da iyaka da zirin Gaza da kuma Isra’ila, kuma Masar ta kasance mai shiga tsakani ta Isra’ila da kungiyoyin Falasdinawa a rikicin da ya faru a baya.

Majiyoyin tsaron Masar sun ce wasu ‘yan yawon bude ido 7,000 sun dawo daga Sinai zuwa Isra’ila tun bayan barkewar fadan.

Haka kuma, Kungiyar agaji ta Red Crescent ta kuma kai agajin jinya zuwa Gaza daga Sinai ta mashigar Rafah.

A ranar Lahadin da ta gabata, an harbe wasu ‘yan yawon bude ido biyu ‘yan Isra’ila da wani jagora dan kasar Masar a wani wurin binciken kayan tarihi da ke birnin Alexandria da ke Arewacin Masar.

Majiyar tsaron ta ce an mika dan sandan Masar din da ake zargi da aikata kisan zuwa kotun soji.

An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na Egypt Air tsakanin Cairo da Tel Aviv har sai yadda hali yayi, yayin da jirage daga Sharm el-Shiekh na kKudancin Sinai zuwa Tel Aviv ke ci gaba da aiki a yau Litinin.

Wannan dai kamar yadda bayanai suka tabbatar ya bai wa Isra’ilawa masu yawon bude ido damar komawa gida, in ji majiyoyin tashar jirgin Saman Masar.

Martanin da muka yi somin-taɓi ne —Netanhayahu

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ci gaba da magana kan matakin da ƙasarsa ta dauka bayan hari mafi muni cikin shekaru da kasar ta fuskanta.

Ƙamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito cewa Natanyahu ya shaida wa jami’an kudancin Isra’ila da ke ziyara, cewa “abin da Hamas za ta fuskanta zai kasance mai matukar muni.”

Netanyahu ya ci gaba da cewa “wannan somin-taɓi ne kawai…duk muna tare da ku kuma za mu fatattake su da karfin tsiya.”

Kwamishina ya yi murabus bayan sauya masa ma’aikata a Kano

Gobara ta ƙone shaguna 50 a kasuwar kara a Sakkwato

An yi canjaras tsakanin Liverpool da Manchester United

Tinubu zai tafi Ghana rantsar da John Mahama