Masar na bukatar taimako saboda rikicin Gaza — EU

Masar na bukatar dauki, don haka ya kamata a taimaka mata.

Masar na bukatar taimako saboda rikicin Gaza — EU

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ya bayyana cewa zai ziyarci Masar a ranar Asabar din nan inda zai yi kira da a tallafa wa kasar da ke kan iyaka da Zirin Gaza da yaki ya daidaita.

A sakamakon barkewar yaki a tsakanin Isra’ila da Hamas a zirin Gaza, Majalisar Tarayyar Turai na yunkurin nema wa Masar talllafin da za a yi amfani da shi wajen agaza wa wadanda iftila’in ya rutsa da su.

“Masar na bukatar dauki, don haka ya kamata a taimaka mata,” inji Michel.

Michel ya yi wannan maganar ce a yayin da yake halartar wani muhimmin taro a Washington tare da shugaban Amurka Joe Biden da kuma shugabar Kwamitin Gudanarwar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen.

Michel ya kuma kara da cewa zai gana da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi a ziyarar da zai kai kasar a karshen mako.

Bugu da kari, a yayin ziyarar, Michel zai halarci taron da Al-Sisi ya gayyace shi wanda za a tattauna batun halin da Gabas ta Tsakiya da Falasdinu ke ciki da kuma hanyoyin samun zaman lafiya.

Da ma dai tun a farkon wannan mako ne Von der Leyen a Tirana ta sanar da cewa za a bude kofar samar da kayan agaji a zirin Gaza.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan