‘Masar na da hannu a harin da aka kai filin jirgin saman Libya’

Mahukunta a Amurka sun bayyana cewa kasar Masar da kuma Haddiyyar Daular Larabawa (UAE) suna da hannu a wani farmaki da aka kai filin jirgin saman babban birnin kasar Libya, Tripoli a karshen makon jiya, wanda aka nufi mayakan Islama masu dauke da makamai .Wani babban jami’i a gwamnatin Amurka ya bayyana wa BBC cewa […]

‘Masar na da hannu a harin da aka kai filin jirgin saman Libya’
‘Masar na da hannu a harin da aka kai filin jirgin saman Libya’

Mahukunta a Amurka sun bayyana cewa kasar Masar da kuma Haddiyyar Daular Larabawa (UAE) suna da hannu a wani farmaki da aka kai filin jirgin saman babban birnin kasar Libya, Tripoli a karshen makon jiya, wanda aka nufi mayakan Islama masu dauke da makamai .
Wani babban jami’i a gwamnatin Amurka ya bayyana wa BBC cewa ba a tuntubi kasarsa ba kafin kai farmakin kuma shammatarsu aka yi.
Rahotanni sun bayyana cewa sojin kasar UAE ne suka kai harin ga ’yan gwagwarmayar a filin jirgin saman birnin Tripoli, inda suka yi amfani da wani sansanin sojin kasar Masar don yin hakan. Kodayake mahukunta a kasar Masar sun musanta hakan, kuma babu wani martani da aka ji kai-tsaye daga kasar UAE.
Sai dai duk da wadannan hare-haren da ake kai wa, ’yan  gwagwarmayar  ba su fice daga birnin Misrata ba da sauran garuruwan kasar da suka kama. Mayakan Islaman suna karkashin wata kungiya ce mai suna Libya Dawn, wadda ta karbe iko da filin jirgin sama  sun bayan hanbarar da gwamnatin marigayi Muhammad Gaddafi  a shekarar 2011. Kodayake masana na cewa kungiyar mayakan na samun goyon bayan kasar katar da Turkiyya, ya yin da a daya bangaren kuma kasashen Saudiyya da Masar da UAE da kuma Amurka suke goyon bayan Janar Khalifa Haftar, wanda ke jagorantar yaki da kungiyon da ke dauke da makamai a kasar.