Masar na tuhumar wakilan Aljazeera 20 da aikata ta’addanci

Gwamnatin Masar na tuhumar ’yan jaridar gidan talabijin na Aljazeeera mutum 20 da zama ’yan kungiyar ta’addanci, inda suke yi kokarin raba kan kasa da tada zaune tsaye, a cewar mai gabatar da kara, wanda ya gurfanar da su.Daga cikin ’yan jaridar da ke aike wa gidan talabijin na aljazera da rahotanni, akwai ’yan kasashen […]

Masar na tuhumar wakilan Aljazeera 20 da aikata ta’addanci
Masar na tuhumar wakilan Aljazeera 20 da aikata ta’addanci

Gwamnatin Masar na tuhumar ’yan jaridar gidan talabijin na Aljazeeera mutum 20 da zama ’yan kungiyar ta’addanci, inda suke yi kokarin raba kan kasa da tada zaune tsaye, a cewar mai gabatar da kara, wanda ya gurfanar da su.
Daga cikin ’yan jaridar da ke aike wa gidan talabijin na aljazera da rahotanni, akwai ’yan kasashen waje mutum hudu, biyu ’yan Birtaniya da dan Austiraliya da dan Holland, wadanda aka zarge su da hada kai da wasu ’yan Masar da ke ba su kudi da bayanai, su kuma su aike da labaran karya, don sanar da duniya cewa kasar ta afka cikin yakin basasa.
Daga cikin mutum 20 da ake zargi da aikata laifin, mutum takwas ne akwai ke tsare, sauran kuwa hukumomi na ta farautarsu. Har yanzu ba a bayyana sunayen wadanda ake tsare da su ba, amma gidan talabijin na Aljazeera ya bayyana sunayen mutum uku, wadanda suka hada da dan kasar Austiraliya, wadanda ya taba zama wakilin BBC a kasar Kanada  Mohamed Adel Fahmy  da Baher Mohamed.
Masar na fama da rikicin siyasa, ga yawan kashe-kashen fararen hula da jami’an tsaro.