Masar ta fara shirin daukar nauyin gasar motsa jiki na yankin Larabawa bayan Maroko ta janye

Yanzu ta tabbata kasar Masar ce za ta dauki nauyin gasar motsa jiki na yankin Larabawa ke shiryawa wanda zai gudana a watan Disamban wannan shekara, bayan kasashen Beirut da Maroko sun janye daga daukar nauyin gasar. Gasar wacce Hukumar shirya wasannin kasashen Larabawa take shiryawa, ta shiga cikin tsaka mai wuya ne bayan kasashen […]

Masar ta fara shirin daukar nauyin gasar motsa jiki na yankin Larabawa bayan Maroko ta janye
Masar ta fara shirin daukar nauyin gasar motsa jiki na yankin Larabawa bayan Maroko ta janye

Yanzu ta tabbata kasar Masar ce za ta dauki nauyin gasar motsa jiki na yankin Larabawa ke shiryawa wanda zai gudana a watan Disamban wannan shekara, bayan kasashen Beirut da Maroko sun janye daga daukar nauyin gasar.

Gasar wacce Hukumar shirya wasannin kasashen Larabawa take shiryawa, ta shiga cikin tsaka mai wuya ne bayan kasashen Beirut da na Maroko sun janye daga daukar nauyinta.
Maroko ta bayar da hujjar ta janye ne daga daukar nauyin gasar saboda wadansu matsaloli da suka yi mata katutu, musamman na tattalin arziki.
Ana sa ran halartar ’yan wasa su kimanin dubu 8 daga kasashe 22 inda za su fafata a wasanni 28.
Shugaban Hukumar shirya wasannin na Oman Sheikh Khalid Ali Zubair ya tabbatar da cewa tuni Masar ta nuna kudurin daukar nauyin gasar a watan Disamban wannan shekara a wata takarda da ta aike wa Hukumarsa da ke alhakin kula da gasar.
Ya ce a makon gobe ne kwamitinsa zai ziyarci Masar don cimma matsaya a kan yadda gasar za ta gudana.
Idan za a tuna, Maroko ce ta janye daga daukar nauyin gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka da aka yi a watan Janairun wannan shekara ana gab da fara gasar saboda matsalar yaduwar cutar Ebola, al’amarin da ya sa Hukumar CAF ta ba Ekuatorial Guinea damar daukar nauyin gasar.