Masar ta rage darajar kudinta
Babban Bankin kasar Masar ya bayyana cewa ya rage darajar kudin kasar da kashi 8.95 cikin 100 wajem musayarsa da Dalar Amurka saboda kalubalen da ake ci gaba da fuskanta a kasar na karancin Dalar.Kamar yadda jaridar Arab News ta ruwaito ranar Litinin, cewa kasar ta kwashe watanni cikin matsalar karancin Dala, inda gabanin matakin […]
Babban Bankin kasar Masar ya bayyana cewa ya rage darajar kudin kasar da kashi 8.95 cikin 100 wajem musayarsa da Dalar Amurka saboda kalubalen da ake ci gaba da fuskanta a kasar na karancin Dalar.
Kamar yadda jaridar Arab News ta ruwaito ranar Litinin, cewa kasar ta kwashe watanni cikin matsalar karancin Dala, inda gabanin matakin babban bankin ake musayar kudin kasar wato Egypt pound 10 da Dalar Amurka guda a kasuwannin bayan fage.
Babban Bankin ya ce matakin zai taimaka wajen samar da daidaito a kasuwannin musayar kudi.
Ya ce matakin zai taimaka wajen maganin matsalar da kasar take fuskanta ciki har da karancin ziyara daga bangaren masu yawon bude ido da kuma masu zuba jari da sauransu.
bangaren yawon bude idon kasar ya sa tattalin arzikin kasar ya samu koma baya saboda rikicin siyasar kasar tun bayan faduwar mulkin tsohon Shugaba Hosni Mubarak a shekarar 2011.
Har ila yau, kakkabo jirgin Rasha da wasu masu tada kayar baya suka yi a yankin Sinai a ranar 31 ga watan Oktoban bara, ya kara jefa tattalin arzikin kasar cikin mawuyacin hali.