Masar ta saki dan jaridar Aljazeera da ta tsare
Hukumoni a Masar sun sallami dan jaridar gidan talabijin din Aljazeera, Abdullah Elshamy wanda ya kwashe wata 10 a tsare.An sallame shi ne ranar Talata bayan da babban mai gabatar da karar ya ba da umarnin hakan bisa halin rashin lafiya da dan jaridar ke ciki.Mista Elshamy wanda ke aiki da bangaren Larabci na gidan […]

Hukumoni a Masar sun sallami dan jaridar gidan talabijin din Aljazeera, Abdullah Elshamy wanda ya kwashe wata 10 a tsare.
An sallame shi ne ranar Talata bayan da babban mai gabatar da karar ya ba da umarnin hakan bisa halin rashin lafiya da dan jaridar ke ciki.
Mista Elshamy wanda ke aiki da bangaren Larabci na gidan talabijin din, ya kasance cikin yajin kin cin abinci saboda yadda aka tsare shi ba tare da tuhuma ba.
A watan Agustan bara ne dai aka kama shi, a lokacin da yake cikin wasu masu zanga-zangar da ke goyon bayan hanbararren shugaba Muhammad Morsi.
Da fari, wata kotun birnin Alkahira ta ce za ta yanke masa hukuncin ne a mako mai zuwa, tare da wasu ma’aikatan Aljazeerar uku wadanda aka kama a watan Disambar bara.
Sauran ’yan jaridar sun hada da: tsohon ma’aikacin kafar hada labarai ta BBC, Peter Greste da Muhammad Fahmy da kuma Baher Muhammad. An dai tsare su ne bisa laifin yada labarai da ba su da sahihanci da kuma laifin taimaka wa kungiyar ’Yan Uwa Musulmi wadda gwamnatin kasar ta bayyana da kungiyar ’yan ta’adda.
Babban mai gabatar da karar ya bukaci a yanke wa ’yan jarida hukuncin shekara 15 ne. Amma daga bisani ya sauya matakin, inda ya umarci a sallami mutum 13 cikin dimbin mutanen da ke tsare.
Mista Elshamy, daya ne cikin mutanen da aka saka. Sauran 12 kuma ’ya’yan kungiyar ’Yan Uwa Musulmi ne.
Gwamnatin Masar ta dakatar da gidan talabijin din Aljazeera wanda ke watsa shirye-shiryensa daga kasar katar, aiki a kasarta bayan ya yada wasu rahotanni da suke goyon bayan hanbararren shugaba Morsi. Amma gidan talabijin din ya musanta wannan zargin a lokuta da dama.