Masar ta sayi jiragen yaki 24 don yaki da mayakan IS a Libiya

kasar Masar ta sayi jiragen sama na yaki 24 don dakile ayyukan mayakan IS a Libiya kasar Masar ta sayi jiragen ne yayin da ta sanya hannu a kan wata kwangila tsakaninta da kasar Faransa, don samar da kayan yaki a kan Dala biliyan 5.2 ciki har da jiragen sama na yaki 24 don fatattakar […]

Masar ta sayi jiragen yaki 24 don yaki da mayakan IS a Libiya
Masar ta sayi jiragen yaki 24 don yaki da mayakan IS a Libiya

kasar Masar ta sayi jiragen sama na yaki 24 don dakile ayyukan mayakan IS a Libiya

kasar Masar ta sayi jiragen ne yayin da ta sanya hannu a kan wata kwangila tsakaninta da kasar Faransa, don samar da kayan yaki a kan Dala biliyan 5.2 ciki har da jiragen sama na yaki 24 don fatattakar mayakan IS.
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da wani gidan rediyo na kasar Faransa a ranar Litinin.
Shugaban ya kuma bukaci majalisar dinkin duniya ta amince a ta tura sojojinta kasar Libiya don a dakile ayyukan mayakan IS.
Ya ce “Ba za mu amince su ci gaba da fille kan ’ya’yanmu ba. Don haka ina kira majalisar dinkin duniya ta tura rundunar sojojinta kasar Libiya don a dakile ayyukan mayakan IS.”
Al-Sisi ya ce a bangarensu za su yi amfani da jiragen yakin wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar Libiya.
Idan ba a manta ba jiragen yakin kasar Masar sun yi ruwan bama-bamai a kan mayakan IS a ranar Litinin, sakamakon wani bidiyo da kungiyar mayakan ta fitar, inda aka nuno ta fille wa Kifdawa kiristoci ’yan kasar Masar 21 kai.
Jiragen sun yi lugudan wutar ne a sansanin mayakan IS da ke kasar Libiya, inda aka lalata wurin da suke horo da kuma ma’ajiyar makaman kungiyar da ke kusa da birnin Derna.
Al-Sisi ya bukaci a samar da isassun makamai, sannan a ba gwamnatin kasar Libiya don a dawo da zaman lafiya a kasar.
Hakan ya sanya majalisar dinkin duniya ta yi taron gaggawa shekaranjiya Laraba, inda aka tattauna yadda za a shawo kan rikicin kasar.