Masar ta yanke hukuncin kisa ga magoya bayan ’Yan uwa Musulmi 188

A shekaranjiya Laraba ne wata kotu a kasar Masar ta yanke wa magoya bayan kungiyar ’Yan uwa Musulmi fiye da 180 hukuncin kisa bayan ta same su da hannu a wani hari da aka kai wani caji ofis din ’yan sanda da ke kusa da birnin Alkahira, ranar 14 ga watan Agustan bara, inda jami’an […]

Masar ta yanke hukuncin kisa ga magoya bayan ’Yan uwa Musulmi 188
Masar ta yanke hukuncin kisa ga magoya bayan ’Yan uwa Musulmi 188

A shekaranjiya Laraba ne wata kotu a kasar Masar ta yanke wa magoya bayan kungiyar ’Yan uwa Musulmi fiye da 180 hukuncin kisa bayan ta same su da hannu a wani hari da aka kai wani caji ofis din ’yan sanda da ke kusa da birnin Alkahira, ranar 14 ga watan Agustan bara, inda jami’an ’yan sanda 11 suka rasa rayukansu. 

Hukuncin ya zo rana daya da jami’an tsaro kasar suka fatattaki masu zanga-zanga goyon bayan kungiyar ’yan uwa Musulmi, inda daruruwa suka rasa rayukansu. Kodayake, kasar tana ci gaba da shan suka kan yadda take murkushe magoya bayan hanbararren Shugaba Mohammed Morsi. Har ila yau, an sha yanke hukuncin kisa da dama ba tare da an aiwatar da shi ba a kasar. Kuma shi kansa wannan hukuncin da aka zartar, ba zai tabbata har sai ya samu amince babban Muftin kasar. Har ila yau, wadanda aka yanke wa hukuncin suna da damar daukaka kara. Fiye da mutum 140 cikin suna tsare ne, sauran kuma an yanke hukuncin ne a bayan idonsu.
Shugaban kungiyar ’Yar uwa Musulmin Mohammed Badie shi ma yana zaman jiran aiwatar masa da hukuncin kisa, bayan wasu shari’u biyu da suka tabbatar da hakan.