Masar za ta hana malamai dubu 55 wa’azi a masallatai

Hukumomin kasar Masar za su hana malaman addini dubu 55 da ba su da lasisi gudanar da wa’azi a masallatan kasar a wani yunkuri na dakile magoya bayan hambararren Shugaban kasar Muhammad Mursi mai ra’ayin Musulunci.Ministan Harkokin Addini na kasar Mohamed Mokhtar Gomaa ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata, a daidai lokacin […]

Masar za ta hana malamai dubu 55 wa’azi a masallatai

Masallacin Al Fatih daya daga cikin masallatan da magoya bayan Mursi suka zauna lokacin zaman dirshan din adawa da juyin mulkin soja Yanzu jami’an tsaro ne ke gadinsa. Hoto daga ReutersHukumomin kasar Masar za su hana malaman addini dubu 55 da ba su da lasisi gudanar da wa’azi a masallatan kasar a wani yunkuri na dakile magoya bayan hambararren Shugaban kasar Muhammad Mursi mai ra’ayin Musulunci.
Ministan Harkokin Addini na kasar Mohamed Mokhtar Gomaa ya bayyana haka a ranar Talatar da ta gabata, a daidai lokacin da aka shiga wata na uku na yunkurin murkushe kungiyar Ikhwanul Muslimina ta magoya bayan Mursi, wanda sojoji suka hambare a ranar 3 ga Yuli.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito Mokhtar Gomaa yana cewa malaman da ba su da lasisin wa’azi ana daukarsu a matsayin masu tsaurin ra’ayin addini kuma barazana ga zaman lafiyar Masar.
Hanin zai shafi kananan masallatai marasa lasisi ko musalla masu yawa. Ya ce, “An dauki matakin ne domin a sanya doka kan yadda ake wa’azi a lokutan Sallar Juma’a, kuma a tabbatar wadanda hukuma ta yarda ne kawai ke wa’azin.”
Mahukuntan kasar dai sun yunkura domin karya kungiyar Ikhwanul Muslimina ne bayan kawar da Shugaba Mursi zababben Shugaba kasa na farko a karkashin tsarin dimokuradiyya a kasar. Fiye da masu kishin Musulunci dubu biyu aka kama aka tsare, mafi yawansu shugabannin Ikhwanu ciki har da Mursi bisa zargin tunzura jama’a su tayar da kayar baya. Kuma wasu daga cikinsu ana zarginsu da ta’addanci ko kisan kai.
An kashe fiye da mutum dubu daya, mafi yawa magoya bayan Shugaba Mursi da suka yi zaman dirshan don nuna adawa da yi masa juyin mulki a wasu tantuna a birnin Alkahira da kuma jami’an tsaro 100.
Gwamnatocin da babu ruwansu da addini a baya, sun yi yunkurin ganin bayan masu wa’azin da suke ganin masu tsaurin ra’ayin addini ne da kuma masallatansu ba tare da sun samu nasara ba, sakamakon tasirin da suke da shi a tsakanin jama’ar kasar.
A can Geneba, kungiyyar Kare Hakkin dam Adam ta Duniya (Amnesty International) ta yi kira a ranar Talatar kan a kafa wani kwamiti mai zaman kansa da zai binciki kisa da musgunawar da jami’an tsaron Masar ke yi ga magoya bayan Ikhwanu.
 kungiyar ta shaida wa Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisar dinkin Duniya a cewa: ‘Juyin mulkin da soja suka yi wa Mursi’ ya “haifar da mugun hautsinin siyasa.” Kuma “A tsakanin 14 da 18 ga Agusta akalla mutum 1, 089 aka kashe, galibi saboda nuna karfi da rashin imani na jami’an tsaro,” kamar yadda wakilin kungiyar a Geneba Peter Splinter ya ce. Ya ce akwai bukatar a gudanar da bincike mai zaman kansa kan take hakkin dan Adam a kasar.
A ranar Litinin Shugaban Hukumar Kare Hakkin dan Adam ta Majalisa, Nabi Pillay ta nanata kiranta na a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan kashe-kashen da kuma bukatarta na a aika wani kwamiti zuwa Masar domin bincikar lamarin.