Masarautar Agege ta nesanta kanta daga masarauta me mulki a jihohi 17
A ’yan makwannin da suka gabata ne Sarkin hausawan Sasa da ke garin Ibadan Alhaji Haruna Mai yasin Sardaunan yamma ya bada sanarwan naɗa sarkin garin Agege da ke Legas a matsayin mataimakinsa a ƙarƙashin masarautarsa da ke mulki a ɗaukacin jihohin kurmi 17 lamarin da masarautar Agegen ta nesanta kanta da shi. A sanarwar […]
A ’yan makwannin da suka gabata ne Sarkin hausawan Sasa da ke garin Ibadan Alhaji Haruna Mai yasin Sardaunan yamma ya bada sanarwan naɗa sarkin garin Agege da ke Legas a matsayin mataimakinsa a ƙarƙashin masarautarsa da ke mulki a ɗaukacin jihohin kurmi 17 lamarin da masarautar Agegen ta nesanta kanta da shi.
A sanarwar da magatakardar masarautar Agege Alhaji Abubakar Aliyu Na’ibi ya fitar a ranar talatar da ta gabata, masarautar ta nesanta kanta da muƙamin mataimakin sardaunan yamma.
Magatakardar masarautar ya ce “Ƙasar Agege tsohuwar alƙarya ce da ’yan kasuwa ’yan Arewa suka kafa bisa dalilin kasuwancin goro a gwanja a ƙasar Ghana da kuma sana’ar saniya da ake kawo wa daga Arewa tun a shekarar 1845, a nan Agege fataken ke yada zango kuma da lokaci ya yi suka kafa sarauta a shekarar 1863 aka sami sarkin Agege na farko. A nan Agege ne turawa suka fara ɗibar soji ’yan asalin Arewa waɗanda ake kiransu jangulobas kafin daga baya su zama sojin Nageriya. Zuwa yanzu anyi sarakuna 7 wanda a cikin su akwai wanda ya yi shekara hamsin a karagar mulki kuma wannan masarautar ta sami takardar shaida daga turawan mulkin mallaka a shekarar 1934, kuma har yanzu muna tafiya a ƙarƙashin tsari na majalisar sarakunan gargajiya na gwamnatin Jihar Legas wanda suma sarakunan Yarbawa ke ciki, domin haka masarauta ce mai tsari da kyakyawar dangantaka da sarakunan mu na Arewa domin mu ne wakilansu a nan kudu, sannan masarauta ce mai tsari da doka kuma bata taɓa zama a ƙarƙashin mulkin wani ba, sai dai a ƙarƙashin dokar Jihar Legas don haka tarihin masarautar mu da asalinta da girman alƙaryarmu ta fi gaban ace wai sarkin ta ya zamo mataimaki ga wata masarauta da ke mulki a wata unguwa,” inji shi.
Da yake wa Aminiya ƙarin haske akan musabbabin abin da ya kai ’yan majalisar sarkin Agege fadar mai martaba sarkin Sasa, cewa ya yi “A lokacin ne Sarkin Sasa yasa aka karanta tarihin sa bayan nan ya nuna mana wata takarda da ke nuna wasu sarakuna sun sanya hanu sun amince masa ya zama shi ne shugaban sarakunan jihohin yamma kaf ɗinta wanda mu babu hannun masarautar mu a ciki, to daga nan ne ya ce ya sanya sarkin mu ya zama mataimakin sa, sai mai martaba sarki ya sanya magajin gari ya yi masa godiya domin ba a baka kyauta ka ƙi karɓa a nan take, amma mu bamu sanda akwai wata masarauta da ke sarauta a jihohin yamma kaf ɗinta ba domin hakan ya saɓa al’ada bamu da wata masarauta kwatankwacin haka a Arewa sannnan a nan kudun babu wani sarkin yarbawa ko na ƙabilar ibo da zai bugi ƙirji ya ce shi ne sarkin sarakunan jihohin yamma ƙaf, don haka bama cikin wannan tsari domin bashi da asali kuma baya kan ƙa’ida. Haka zalika maganar da aka yi cewa masarautar mu ta kai wani mutum fadar sarkin Sasa a naɗa shi sarauta ba daidai bane, mu ta’aziyace ta kai mu ko da muka je can mun iske sarkin hausawan Idiyarba da na Ikotu bamu sani ba ko sune suka je neman sarauta domin su ne suka yi shekuru 30 tare da sarkin Sasa amma mu laƙarmu da shi ta shekara biyu ne, muna da masarautar mu mai asali babu abin da zai sa mu kai wani namu mune ma masa sarauta a wata masarauta,” inji shi.
Ɗan Iyan Agege ya ƙara da cewa “Sarkin Sasa ya aiko wa masarautar Agege da takar da ba a bisa tsari da ƙa’ida da muke gudanar da sarauta ba, sarkin Agege ya nuna mana cewa shi a matsayin sa na Sardaunan yamma in ya bai wa wani sarautar sarkin yamma hakan na nufin shi ma zai koma ƙarƙashinsa ke nan, domin ai shi sarki gaba yake da sardauna, nan take Sarkin Agege ya bani umarni na je fadar Sasa na yi masa bayanin illar hakan, nan take ya gane ya yi murna ƙwarai sannan ya ce duk sanda zai naɗa sarauta a Agege zai nemi shawarar mu. Bugu da ƙari bamu da wata matsala da Alhaji Sama’ila sai dai ya yi wa masarauta Agege laifi a baya wanda shi ne ya sanya sarkin Sasa ya turo shi ya nemi afuwa, sai dai daga bisani ya ce bai yi laifin komai ba, to laifin da ya yi wa masarautar Agege shi ne yana amfani da sunan sarki tun a baya domin kowa ya fi saninsa da Sama’ila Sarki baya ga haka a matsayin sa na ɗan Agege bai taɓa zuwa fada ya yi gaisuwa ga sarki ba ko ya haɗu da shi a wajan taro ya kai masa gaisuwa bai taɓa yin haka ba, baya ga wannan wannan suna na sarki da yake amfani da shi a watan azumin nan da ya gabata jami’an ’yan sanda daga hedikwatar su ta Abuja sun zo da takardar sammaci tare da wasu mutane suka zo fada wai an basu takardar sanmmaci su kama sarki, nan Sarkin Agege ya fito zai je masalacin juma’a sai ga jami’an tsaro sun zo suka same shi wai ance su tafi da shi ga takardar sammaci, a cikin su ne wani mutum ya ce ba wannan bane wanccan sarkin ba shi da yawan shekaru kamar wannan sannan yana da tsagu uku-uku to a haka ne suka tafi suka kyale shi. Sannan mu ba ma adawa da wani mutum, don haka muna masa murna da sarautar da aka naɗa shi, sai dai abin da ya kamata ya sani shi ne, a dokokin masarautar Agege wani baya zuwa wani gari ya je ya karɓo sarauta sannan ya zo Agege ya kafa fada ya fara yin yin shara’a ko makamancin haka, domin ba zamu yarda wani ya raba mana kan jama’ar mu ba,” inji ɗan iyan Agege.
Jihar Legas ta daɗe tana fama da matsalar tsarin shugabanci a masarautun gargajiya, inda a cikin garin Legas ake da Sarakunan hausawan Legas biyu wanda ko wannen su ke amsa sunan sarkin Legas, kuma ko wannen su ke naɗa masu anguwanni da hakimansa hakan ne yasanya a wurare da dama ake da sarki biyu, kamar sassa cikin garin Legas, da Idiyarba da makamantan haka, garin Agege ne kaɗai ke amsa Sarkin hausawan Agege ɗaya kuma shi ne ya kuɓuta daga rikicin masarautun gargajiya baya ga wannan na baya-bayan nan da yake so ya kunno kai.