Masarautar da ta shafe shekara15 babu sarki

Al’ummar gundumar Itede da ke Karamar Hukumar Ado Odo/Ota a Jihar Ogun sun yi wa ofishin gwamnan jihar kawanya suna bukatar a nada musu sabon sarki. Mazauna yankunan sun yi zanga-zangar ne karkashi jagorancin dagattansu (Baale) da sauran shugabannin yankin, kan rashin basaraken na tsawon shekara 15 wanda suka ce ya kawo musu koma baya. […]

Masarautar da ta shafe shekara15 babu sarki

Al’ummar gundumar Itede da ke Karamar Hukumar Ado Odo/Ota a Jihar Ogun sun yi wa ofishin gwamnan jihar kawanya suna bukatar a nada musu sabon sarki.

Mazauna yankunan sun yi zanga-zangar ne karkashi jagorancin dagattansu (Baale) da sauran shugabannin yankin, kan rashin basaraken na tsawon shekara 15 wanda suka ce ya kawo musu koma baya.

Masu zanga-zangar sun rika daga kwalaye dauke da rubuce-rubuce kamar, “Al’ummar Itele masu son zaman lafiya ne”; “Babu Ademola, babu sarki”; “Garin da babu sarki fatalwar gari ne”; “Jama’ar Itele sun cancanci a nada musu sarki”; da sauransu.

Da yake jawabi a madadin jama’ar, daya daga cikin dagattan masarautar, Cif Oluyemi Onifade ya sahida wa ’yan jarida cewa a kwanan nan masu zabar sarki a masarautar suka zabi Yarima Ademola Asorota a matsayin sabon sarki.

Sai dai ya ce gwamnatin ta dade tana jan kafa wajen nada sabon sarkin.

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin da ta gaggauta nada shi, yana mai gargadin cewa duk wani yunkuri na canza abun da aka zaba zai iya tayar da zaune tsaye.

Da yake wa masu zanga-zangar jawabi a madadin gwamnan jihar, Daraktan Al’amuran Masarautu da Kananan Hukumomi, Adesoji Adewuyi ya amince cewa an samu tsaiko wajen nada sarkin.

Sai dai ya ce tuni suka mika batun ga Ma’aikatar Shari’a domin ba wa gwamnatin shawara kan abin da ya kamata ta yi.

Ya kuma tabbatar wa masu zanga-zangar cewa gwamnati za ta tabbatar an yi abin da ya kamata domin kauce wa rikici.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7