Masarautar Dutse ta dakatar da dan Sule Lamido daga hakimci

Masarautar Dutse da ke Jihar Jigawa ta dakatar da dan tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido, wato Alhaji Mustapha Sule Lamido daga sarautarsa ta Hakimin Bamaina kuma Santurakin Dutse.Mustapha da dan uwansa Aminu da kuma mahaifinsu Alhaji Sule Lamido suna fuskantar shari’a kan zargin sace biliyoyin Naira mallakar gwamnatin Jihar Jigawa.Wata sanarwa mai lamba ECD/69/bOL […]

Masarautar Dutse ta dakatar da dan Sule Lamido daga hakimci
Masarautar Dutse ta dakatar da dan Sule Lamido daga hakimci

Masarautar Dutse da ke Jihar Jigawa ta dakatar da dan tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Sule Lamido, wato Alhaji Mustapha Sule Lamido daga sarautarsa ta Hakimin Bamaina kuma Santurakin Dutse.
Mustapha da dan uwansa Aminu da kuma mahaifinsu Alhaji Sule Lamido suna fuskantar shari’a kan zargin sace biliyoyin Naira mallakar gwamnatin Jihar Jigawa.
Wata sanarwa mai lamba ECD/69/bOL III/1060, mai kwanan wata 31 ga Janairu, 2016 dauke da sanya hannun da Sakataren Masarautar Dutse Alhaji Yunusa Garba,  ta ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take.
Takardar ta ce: “Sakamakon umarni da Mai martaba (Sarkin Dutse Alhaji Muhammadu Nuhu Sanusi) ya samu daga ofishin Sakataren Gwamnatin Jiha, mai lamba SSG/AF/S/A/14/bOL III/82 ta ranar 19 ga Rabi’ul Akhir 1437 Bayan Hijira daidai da 29 ga Janairun, 2016, ana sanar da kai an dakatar da kai daga sarautarka nan take.”
A cewar sanarwar daukar matakin ya dogara ne da sashi na 04301 da sashi na 04412 na dokokin aikin gwamnati bisa lura da shari’ar ta shafi Mustapha da mahaifinsa a wata Kotun Tarayya da ke Abuja.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan lamarin Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa Alhaji Abdulkadir Fanini ya ce sun bai wa masarautar umarnin dakatar da Hakimin na Bamaina ne saboda suna fuskantar shari’a a gaban kotu.
Ya ce da zarar kotu ta wanke su ba a same su da laifi ba za a iya mayar da su sarautarsu ya ci gaba da yin hakimcinsa.
Alhaji Fanini ya ce dakatar da hakiman hurumi ne na gwamnatin jiha, masarauta ba ta da ikon dakatar da hakimi sai da yawun gwamnatin jiha, dagaci ko mai unguwa ne kai-tsaye masarauta take da ikon cirewa ko dakatarwa.
Sakataren Gwamnatin Jihar ya musanta cewa gwamnatin jihar tana yi wa dan tsohon Gwamnan bi-ta-da kulli ne saboda bambancin siyasa.
Ya ce babu batun maganar siyasa a cikin lamarin, laifi ake zarginsu da aikatawa kuma suna gaban kotu, kuma laifin da ake zarginsu babban laifi ne da dokar kasa ta ce a dakatar da duk wanda ake zargi da irinsa daga mukaminsa sai an kammala shari’a.
 Umarnin dakatarwar ta hada da Hakimin Kiyawa kuma Dokajen Dutse Alhaji Wada Abubakar.