Masarautar Dutse ta raba Zakkar Naira miliyan 3 da dubu 700

Masarautar Dutse a karkashin Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ta hannun Hakimin Dutse, Alhaji Jamilu Basiru Sunusi Turakin Dutse ta raba wa marasa karfi da nakasasu 368 Zakkar Naira miliyan uku da dubu 700. An gabatar da rabon Zakkar na bana ne a fadar Hakimin Dutse a ranar Larabar makon jiya.A jawabin […]

Masarautar Dutse ta raba Zakkar Naira miliyan 3 da dubu 700
Masarautar Dutse ta raba Zakkar Naira miliyan 3 da dubu 700

Masarautar Dutse a karkashin Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ta hannun Hakimin Dutse, Alhaji Jamilu Basiru Sunusi Turakin Dutse ta raba wa marasa karfi da nakasasu 368 Zakkar Naira miliyan uku da dubu 700.

An gabatar da rabon Zakkar na bana ne a fadar Hakimin Dutse a ranar Larabar makon jiya.
A jawabin Mai martaba Sarkin Dutse a lokacin rabon Zakkar ya yaba wa masu karbo Zakkar da wadanda suke bayar da ita a duk shekara saboda hadin kan da suke ba masarautar, kuma ya hori jama’a su ji tsoron Allah wajen tsayawa su fidda hakkin Allah da ya rataya a wuyansu.
Ya kuma bukaci malamai su ci gaba da fadakar da jama’a muhimmancin fitar da Zakka domin rashin fitar da ita na daya daga cikin abubuwa da suke haifar da aukuwar masifu a bayan kasa.
Wani malami da ya yi jawabi a wajan rabon Zakkar Ustaz Aliyu Galamawa ya shawarci jama’a musamman masu hannu da shuni su yi koyi da irin aikin Allah da masarautar Dutse ta gabatar, inda ya ce Zakkar an tara ta ne a iyakacin masarautar kuma an raba ta ne ga jama’ar yankin da aka tara ta.
daya daga cikin wadanda suka amfana da Zakkar wadda dan kabilar Ibo ne mazaunin Dutse mai suna Fedelis ya ce Hakimin Cikin-gari ne ya ba da sunansa a matsayin wadanda za su amfana da Zakkar. Ya ce ba komai ya sa haka ba illa kauna da zaman lafiya da yake yi da jama’ar yankin.
Ya ce duk da cewa Zakka aba ce da ta rataya a wuyan Musulmi, shi ma yana bayar da tasa gudunmawar wajen taimaka wa Musulmi marasa karfi ta hanyar tallafa musu da magani kyauta a lokacin da suka je kantin maganinsa sayen magani.
Fedelis ya ce ya ba kowa ya fi ba, amma kaunar da ake masa ya sa karamar Hukumar Dutse ta sanya shi daya daga cikin masu ba Shugaban karamar Hukumar Dutse shawara duk da cewa yana sana’a hakan bai hana masarautar Dutse ta cire sunansa daga cikin masu amfana da Zakkar ba.