Masarautar Fika ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a Potiskum

Gasar ta bana ta samu halartar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa 64 daga ƙananan hukumomi huɗu.

Masarautar Fika ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a Potiskum

Masarautar Fika da ke Jihar Yobe ta buɗe gasar ƙwallon ƙafa karo na uku a filin wasa na Dabo Aliyu da ke garin Potiskum.

An buɗe gasar ƙarƙashin jagorancin mai martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe.

Gasar wacce aka fara a shekarar 2011 ta bunƙasa zuwa wani gagarumin taron wasanni a yankin, wadda ke haɗa ƙungiyoyi daga ƙananan hukumomi huɗu na yankin da suka haɗa da Fune, Potiskum, Fika, da Nangere.

A shekarar 2017 aka gudanar da gasar karo  na biyu, lamarin da ya ƙara tabbatar da gasar a matsayin ɗaya daga cikin manyan wasannin ƙwallon kafa a jihar.

A wannan shekarar ta 2025 an buɗe gasar ce da wasa tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Total Pillars FC Potiskum da Parma FC ita ma a garin na Potiskum.

Ƙungiyoyin biyu dai sun ƙare zagayen farko ba tare da an zura ƙwallo a raga ba, amma ana minti 19 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Abdulzabi na Parma ya zura ƙwallo daya tilo da aka tashi a wasan, inda ƙungiyar tasa ta samu nasara da ci 1-0.

Gasar ta bana ta samu halartar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa 64 daga ƙananan hukumomi huɗu da suka shiga gasar.

Wani muhimmin abin da ya fi ɗaukar hankali a bikin buɗe gasar shi ne bayar da lambobin yabo ga fitattun mutane domin nuna irin gudunmawar da suke bayarwa wajen wasanni da ci gaban al’ummar wannan masarauta ta Fika.

Waɗanda aka karrama sun haɗa da Alhaji Garba Mohammed, FIFA Lamido, Aliyu Abba Bulama (AFCON), Sadik Rabiu Alkali da Alhaji Ba’aba Abba (Aljino na Fika).

Ana sa ran za a ci gaba da gudanar da gasar nan da makonni masu zuwa, inda za a haɗa haziƙan ’yan ƙwallon ƙafa da masu sha’awar ƙwallon ƙafa daga sassan yankin na Masarautar ta Fika.

Mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Muhammad Ibn Abali Muhammad Idris ya yi fatan alheri ga waɗanda suka samu damar shiga wannan gasa tare da yi musu addu’ar kammala gasar lafiya.