Masarautar Gwandu za ta taimaka game da karbar katin zama dan kasa

Masarautar Gwandu da ke Jihar Kebbi ta sha alwashin ba da tata gudunmawa wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin karbar katin shaidar zama dan kasa. Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ne ya bayyana haka a lokacin da yake karbar nasa katin, wanda aka kaddamar da ba da shi a fadarsa ta […]

Masarautar Gwandu za ta taimaka game da karbar katin zama dan kasa
Masarautar Gwandu za ta taimaka game da karbar katin zama dan kasa

Masarautar Gwandu da ke Jihar Kebbi ta sha alwashin ba da tata gudunmawa wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin karbar katin shaidar zama dan kasa.

Mai martaba Sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ne ya bayyana haka a lokacin da yake karbar nasa katin, wanda aka kaddamar da ba da shi a fadarsa ta Abdullahi Fodiyo da ke Birnin Kebbi fadar jihar.
Sarkin na Gwandu ya ce wannan katin yana da muhimmanci domin duk kasar da mutum ya je ya nuna shi ya nuna cewa shi cikakken dan Najeriya ne, kuma gwamnati ta san da zamansa ba za a yi masa wulakanci ba, mudddin ya shiga kasar bisa doka.
Sarkin ya ce dole ne ’yan Najeriya su zage dantse domin ganin sun mallaki katin, inda ya ce masarautarsa za ta hada hannu da sauran masarautun jihar da hukumar bada katin dan kasar domin ganin al’umma sun karbi katin.
Ya yi kira ga ma’aikatar hukumar su tabbatar da duk wanda ya zo don a yi masa katin an yi masa babu tare da nuna bambancin kabila ko addini ba, domin katin ba ya da alaka da siyasa.
Tunda farko a jawabin shugaban hukumar a Jihar Kebbi, Alhaji Ahmad Umar ya shaida wa Sarkin cewa hukumarsa ta soma rarraba katunan dan kasa, amma har yanzu akwai bukatar mutane su fito domin a yi musu rajista, wadanda suka yi kuma su hanzarta zuwa sakatariyar hukumar domin su duba sunayensu don su karba. Ya nemi masarautar Gwandu ta taimaka wurin wayar da kan jama’a kan muhimmancin katin.