Masarautar Kano ta dakatar da Dagacin Kawo

Masarautar Kano ta bayar da sanarwar dakatar da Dagacin Kawo Malam Kabiru Garba da yayansa da kannensa shida wadanda dukkaninsu masu unguwanni ne a Kano. Masarautar ta ce ta dauki wannan mataki ne a kan Dagacin saboda korafin da wani mazaunin unguwar Kawo, Salisu Abbas ya yi gabanta cewa Dagacin ya sanya ’ya’yansa da kannensa […]

Masarautar Kano ta dakatar da Dagacin Kawo
Masarautar Kano ta dakatar da Dagacin Kawo

Masarautar Kano ta bayar da sanarwar dakatar da Dagacin Kawo Malam Kabiru Garba da yayansa da kannensa shida wadanda dukkaninsu masu unguwanni ne a Kano.

Masarautar ta ce ta dauki wannan mataki ne a kan Dagacin saboda korafin da wani mazaunin unguwar Kawo, Salisu Abbas ya yi gabanta cewa Dagacin ya sanya ’ya’yansa da kannensa sun yi masa dukan kawo wuka inda har suka fasa masa kai.
Kafin masarautar ta yanke wannan hukunci sai da ta nemi shaidu mutum biyu kuma ’yan uwa ne ga Dagacin inda suka tabbatar da cewa Dagacin ya aikata laifin da ake zarginsa da shi.
Sarkin Kano Malam Muhamamdu Sanusi II ya ce masarautarsa ba za ta yarda wani shugaba ya rika zalunta ko cin zarafi ko wulakanta talakawansa ba.
Rahotanni sun ce Dagacin da masu unguwannin za su iya rasa rawunansu idan har kwamitin binciken da masauratar ta kafa a kan lamarin ya kama su da laifi.
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin Dagacin amma ya ki cewa komai.
Sai dai mai korafin Malam Salisu Abbas ya yi godiya ga masarautar inda ya bayyana ta da cewa ita ce gatan marar gata.
Majiyarmu ta ce a karshen makon jiya ne Dagacin tare da yayansa suka yi wa magidancin mai suna Salisu Abbas duka sakamakon wata ’yar hatsaniya da ta shiga tsakaninsu.
An ce tun dadadewa akwai jikakkiya tsakanin Malam Salisu da Dagacin wadanda makwabtan juna ne inda sai da ta kai su ga gurfana gaban hukuma.