Masarautar kasar Maroko ta gayyaci Sarkin kano ziyarar kwana 7
Sarki kuma Shugaban Kasar ne ya gayyaci Sarkin na Kano
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero zai gana da Sarki Hassan II na kasar Maroko a wata ziyarar aiki da sarkin yake yi a kasar.
Sarki Muhammad na VI kuma Shugaban Kasar ne ya gayyaci Sarkin na Kano don wannan ziyara ta kwanaki bakwai.
A ranar Asabar ce Sarki Aminu Bayero shi da tawagarsa suka sauka a kasar, inda aka yi musu tarba ta musamman.
Yayin ziyayar, ana sa ran sarkin na Kano zai gana da Sarki kuma Shugaban Kasar na Maroko, inda za su tattauna muhimman abubuwan da suka shafi kasashen biyu.
Akwai daddaddiyar alaka ta kasuwanci a tarihi a tsakanin Kano da kasar Maroko wacce ta samo asali tun lokacin da ake fatauci a zamanin kakannin sarakunan biyu.