Masarautar Katsina ta dakatar da Hakimai biyu

Masarautar Katsina ta dakatar da hakimai biyu a lardin da suke jagoranta. Sakataren masarautar, Sallama Katsina, Bello Ifo ne ya fitar da sanarwar. Wadanda aka dakatar din su ne: Hakimin Jikamshi, Alhaji Aminu Kabir Usman (Durbin Katsina) da Hakimin Kaita, Alhaji Abdulkarim Kabir Usman (Sarkin Sullubawan Katsina). Bello, ya ce an kafa kwamitin da zai […]

Masarautar Katsina ta dakatar da Hakimai biyu

Masarautar Katsina ta dakatar da hakimai biyu a lardin da suke jagoranta. Sakataren masarautar, Sallama Katsina, Bello Ifo ne ya fitar da sanarwar.

Wadanda aka dakatar din su ne: Hakimin Jikamshi, Alhaji Aminu Kabir Usman (Durbin Katsina) da Hakimin Kaita, Alhaji Abdulkarim Kabir Usman (Sarkin Sullubawan Katsina).

Bello, ya ce an kafa kwamitin da zai binciki laifin da suka yi na rashin da’a, wanda ya yi sanadiyyar dakatar da Hakiman biyu.