Masarautar Saminaka ta sasanta ’yan Shi’a da ’yan darika kan masallacin Juma’a

Masarautar Saminaka a Jihar Kaduna ta sasanta matsalar da ta taso a tsakanin ’yan Shi’a da ’yan darika kan irin abubuwan da ’yan Shi’ar gudanarwa a babban Masallacin Juma’a na garin Saminaka. Masarautar ta sasanta wannan matsala ce a wani taro da aka gudanar a fadar Sarki wanda ya kunshi bangarorin biyu da Hakimin Rahaman […]

Masarautar Saminaka ta sasanta ’yan Shi’a da ’yan darika kan masallacin Juma’a
Masarautar Saminaka ta sasanta ’yan Shi’a da ’yan darika kan masallacin Juma’a

Masarautar Saminaka a Jihar Kaduna ta sasanta matsalar da ta taso a tsakanin ’yan Shi’a da ’yan darika kan irin abubuwan da ’yan Shi’ar gudanarwa a babban Masallacin Juma’a na garin Saminaka.
Masarautar ta sasanta wannan matsala ce a wani taro da aka gudanar a fadar Sarki wanda ya kunshi bangarorin biyu da Hakimin Rahaman Saminaka da Hakimin Saminaka da manyan gari da jami’an tsaro a ranar Alhamis din makon jiya.
’Yan darika da suke da masallacin ne suka koka ga fadar Sarkin kan irin abubawan da ’yan Shi’a ke yi a masallacin da suka hada da wa’azi bayan Sallar Juma’a da tarurrukan maza da mata da fareti da kada badujala a masallacin da kuma zagin sahabbai, inda suka ce wadannan abubuwa sun saba wa fahimtarsu.
Bayan wannan koke ne Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya dakatar da ’yan Shi’ar daga yin tarurruka a masallacin, har zuwa lokacin da aka sasanta su da ’yan darikar.
Da yake yiwa wakilinmu karin bayani kan taron da Sarkin ya kira don warware matsalar, dan Makwayon Saminaka Malam Ahmed Tijani ya ce an tattauna abubuwa biyar da ’yan Shi’ar suke yi a masallacin, kuma sun amince za su cire taron mata da maza da suke yi da fareti da kada badujala  a masallacin.
Amma an amince su ci gaba da yin taron wa’azin bayan Sallar Juma’a da taron da suke yi a ranar Talata a masallacin.
Ya ce Sarkin ya samu nasarar warware matsalar, don haka ya yi kira ga al’ummar yankin su ci gaba da zaman lafiyar da aka sansu da ita.
Da yake zantawa da wakilinmu kan al’amarin, Babban Limamin Saminaka, Imam Shu’aibu Liman Saminaka ya ce taron ya yi kyau, ya ce suna son zaman lafiya a yankin, kuma babu wani tashin hankali da za a yi kan wannan lamari. Sai ya yi fatar za a yi aiki da yarjejeniyar da aka cimma a taror.
Jagoran ’yan Shi’a na yankin Saminaka Malam Yusufu Abubakar ya ce zaman ya yi kyau kwarai da gaske. Ya ce dama wannan matsala ba daga wajensu ba ne, domin duk wanda ya san almajiran Sheikh Ibrahim Zazzaky ya san mutane ne masu tafiya kan tsari.
Ya ce yaran da suka rubuta takardar koke kan abubuwan da suke yi a masallacin wasu kannensu ne wasu ’ya’yansu ne. Kuma malaman da suka yi zaman da su yawancinsu malamansu ne.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi