Masarautar Tibi ta ja daga da makiyaya

Tor Tib na Jihar Biniwai, Dokta Alfred Akawe Torkula ya ce ba zai bayar da ko da inci guda na wani fili da ke karkashin masarautarsa ga Fulani makiyaya domin yin kiwon dabbobinsu ba.Basaraken ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Godwin Ber a lokacin da ake wani taron al’ummar Tibi a […]

Masarautar Tibi ta ja daga da makiyaya
Masarautar Tibi ta ja daga da makiyaya

Tor Tib na Jihar Biniwai, Dokta Alfred Akawe Torkula ya ce ba zai bayar da ko da inci guda na wani fili da ke karkashin masarautarsa ga Fulani makiyaya domin yin kiwon dabbobinsu ba.
Basaraken ya bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunsa, Godwin Ber a lokacin da ake wani taron al’ummar Tibi a karshen makon jiya. Ya yi nuni da cewa ba daidai ba ne al’ummar Tibi su bayar da wurarensu domin kiwo saboda yadda su ma suke samun bunkasar yawan jama’a, wanda ya sanya bukatar kasar noma ta karu a masarautar.
“A karkashin ikona, ba zan iya bayar da ko da inci daya na kasar Tibi ga Fulani makiyaya don gudanar da kiwon dabbobinsu ba . Jama’ar da nake wakilta manoma ne kuma su ma suna bukatar wadatacciyar kasar noma.  Yadda ake yi a kasashen da suka cigaba shi ne, makiyayi na killace dabbobinsa ne a wani fili da ya tanada da kudinsa don gudanar da ayyukan kiwo. Daga nan ne kuma sai ya tanadar da abincin da za su ci. Wannan shi ne maganin tashe-tashen hankulan da ke faruwa tsakanin manoma da Fulani makiyaya.” Inji shi.
Ya kara da cewa, tsarin kiwon da Fulani ke bin burtali don sama wa dabbobinsu abinci, tsohon yayi ne, kuma ya kamata a yi watsi da shi. Basaraken ya ce, kebe wadansu wurare don kiwon dabbobin makiyaya ba zai warware matsalar tashe-tashen hankula tsakanin Fulani da manoma a jihar ba.
“Noma ne sana’armu kuma muna fama da karancin kasar noma. Ana ci gaba da karbe kasar noman jama’armu da ke jihohin Taraba da Nasarawa. Da wannan suke so mu ma mu bayar da tamu kasar? Hakan ba za ta sabu ba.” Inji shi.
Da yake mayar da martani, Sakataren kungiyar Fulani makiyaya (Miyetti Allah), reshen Jihar Binuwai, Malam Garus Gololo ya ce mambobin kungiyar ba za su yi rikici da kowa saboda karbe musu wuraren kiwo ba, sai dai ya bukaci Tor Tib da ya yi hakuri ya sauya wannan matakin nasa, albarkacin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin al’umomin biyu.
Ya ce: “Muna ba shi hakuri tare da bukatarsa da ya manta da duk wani rikici da ya faru tsakaninmu da al’ummar Tibi a baya, domin hakan ne kawai zai farfado da tsohuwar dangantarkar da ke tsakaninmu, wanda har ta kai ga ana samun auratayya a tsakaninmu. Saboda haka ne muke ba basaraken hakuri tare da ba shi tabbacin cewa ba za mu kara tada zaune-tsaye ba a masarautarsa”. Inji shi.
Shi kuwa tsohon Shugaban kasa, Janar Yakubu Gawon nuni ya yi da cewa, ya yi amannar cewa ba Fulani makiyaya ba ne ke kai wadannan hare-haren, saboda a cewarsa, yawancinsu yara ne. Ya ce wadansu ne suke shiga irin ta Fulani don cimma bukatunsu.
Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin wani taron addu’a da ya jagoranta a Jihar Ebonyi, ranar Asabar da ta gabata. Inda kuma ya bukaci ’yan Najeriya da su cigaba da yin addu’a don ita ce kawai za ta taimaka wajen kawo karshen wadannan masalolin tsaron.