Masarautar Zazzau ta dakatar da Hakimi kan zargin lakada wa matashi duka
Ana zargin Hakimin ne da sa wa a lakada wa wani matashi duka
Majalisar Masarautar Zazzau ta dakatar da Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah daga kujerarsa ta Marafan Yamman Zazzau.
Masarautar ta ce daukar matakin ya biyo bayan koken da al’umman Unguwar Magajiya da ke birnin Zariya suka mika, na zargin cin zarafin wani mutum da ake yi wa basaraken.
- Jirgin farko na Alhazan Najeriya ya taso
- Ali Ndume, Rufa’i Hanga sun zama jagororin Majalisar Dattawa
A takardar sanarwar da mai magana da yawunta, Abdullahi Aliyu Kwarbai ya fitar ranar Talata, masarautar ta ce ta amince cikin gaggawa ta dakatar da Hakimin har sai abin da hali ya yi a nan gaba.
Shi dai Alhaji Mustapha, majalisar ta same shi ne da laifin zartar da hukunci kan wani Yusuf Yahaya mazaunin Unguwar Magajiya wanda a bisa doka ba shi da ba shi da damar yi ko daukan haka, a cewar sanarwar.
Masarautar ta kuma jawo hankalin dukkan Hakimai da Dagatai da sauran masu rike da sarautar gargajiya cewar ba ta amince da su rinka daukar doka a hannunsu ba.
Majalisar Masarautar ta umarci masu rike da sarautu da su kiyaye cewan ba za ta lamunce da cin zarafi ko tozarta kowane irin jinsi na al’umma ba. Ta kuma kara jawo hankalin da a rinka mika wadanda ake tuhuma bisa laifuka ga mahukunta.
Majalisan Masarautar ta kuma tabbatar wa al’umma cewar a shirye take domin daukar mataki mai tsanani ga duk wanda ya sabawa dokokin da shari’a ta shimfida.
Sai dai da yake mayar da martani kan dakatarwar, Alhaji Mustapha Adamu Ubaidullah ya ce ya sa an daki shi wanda ake zargin ne saboda ya kama shi yana luwadi da wani yaro a bayan gidansa.
Ya kuma zargi wasu ’yan majalisar Sarki da hannu wurin ta’azzara wannan rikicin.
A cewar shi, ya dauki wannan matakin ne don gudun bata sunan shi da na Sarkin Zazzau.
Ya bukaci a gabatar da shi ga hukuma maimakon dakatar da shi da aka yi kawai, ba tare da binciken abin da ya sa ya dauki wannan matakin ba.
Dan haka wannan matakin da aka dauka an biyewa son zuciyar wasu ne kawai, a cewarsa.