Masarautar Zazzau ta soke hawan Babbar Sallah

Ba za yi hawan ba ne saboda Sarki ya tafi Saudiyya

Masarautar Zazzau ta soke hawan Babbar Sallah

Gidan sarautar Zazzau

Masarautar Zazzau ta sanar da soke bikin Hawan Babbar Sallah na bana da aka saba yi kowacce shekara.

Sakataren masarautar, Mallam Yusuf Abubakar Hayat, ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya sanya wa hannu mai dauke da kwanan watan 12 ga watan Yuni, 2023.

Sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan tafiyar da Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli ya yi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da Aikin Hajjin bana.

Idan za a iya tunawa, a kwanan nan ne Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya nada Sarkin a matsayin Amirul Hajji na jihar a kasa mai tsarki a bana.

A sakamakon sokewar dai, yanzu al’ummar masarautar da makwabta ba za su sami damar kallon ba kamar yadda suka saba.