Masarautun Binji da Oto Awori sun bai wa Sarkin kasuwar Alabar Rago mukami

Masarautun Binji a Jihar Sakkwato da Oto Awori a Jihar Legas, sun nada Sarkin Kasuwar Alabar Rago, Alhaji Umaru Nagwaggo Sakkwato, a matsayin Dikkon Binji da Bobaselu na Oto Awori, a bukukuwan da aka gudanar a Binji da Oto Awori, a lokuta daban-daban a makon jiya. Jim kadan bayan kammala bikin Legas, wakilinmu ya tattauna da […]

Masarautun Binji da Oto Awori sun bai wa Sarkin kasuwar Alabar Rago mukami
Masarautun Binji da Oto Awori sun bai wa Sarkin kasuwar Alabar Rago mukami

Masarautun Binji a Jihar Sakkwato da Oto Awori a Jihar Legas, sun nada Sarkin Kasuwar Alabar Rago, Alhaji Umaru Nagwaggo Sakkwato, a matsayin Dikkon Binji da Bobaselu na Oto Awori, a bukukuwan da aka gudanar a Binji da Oto Awori, a lokuta daban-daban a makon jiya.
 Jim kadan bayan kammala bikin Legas, wakilinmu ya tattauna da Alhaji Umaru Nagwaggo don jin yadda sarautun biyu suke. “Sarautar Dikko ta Fulani ce, duk da yake mahaifina da kakana ba su rike wannan sarauta ba,  amma mun yi gadon ta ne daga kakanni da suka yi zama tare da marigayi Shehu Usman danfodiyo. Duk mai rike da ita, zai iya gayyatar Fulanin jihar baki daya domin tattaunawa game da matsalolin da suke fuskanta da samo hanyoyin ci gabansu, musamman zamantakewarsu da sauran jama’a. Na amince da karbar sarautar ce domin bayar da tawa gudunmawa ga ci gaban Fulanin Binji da al’ummar Jihar Sakkwato da kasa baki daya”. Inji shi.
 Sai dai Alhaji Umaru ya ce zamansa a masarautar Binji bai zama dole ba, musamman dayake an samu kungiyoyin Fulani kamar Miyetti Allah, wacce take gudanar da yawancin abin da mai rike da sarautar zai yi.
Ya ce, “Duk da ina zaune nesa, a matsayin wakilin sarkin gari zan ci gaba da tuntubar su a kowane lokaci da bayar da muhimman shawarwari da tsawatarwa a tsakanin Fulani, kuma in Allah Ya yarda, zan cimma burina kan haka. Fulani mutane ne masu juriya da sanin ya kamata da kawaici da kunya, saboda haka ba zan samu matsala wajen kyautata hulda tsakanina da su ba”.  
A game da sarautar Bobaselu da masarautar Oto Awori ta nada shi, Alhaji Umaru ya ce, “daukacin Yarbawa da Hausawa da Ibo da sauransu da suke gudanar da harkoki a cikin kasuwar Alabar Rago, sun isa shaida a game da irin jagorancin da nake yi musu ba tare da bambanci ba. Ina da sha’awar ganin kowa ya samu ’yanci kuma ina kwatanta adalci gare su ba tare da neman wani abu wurin kowa ba. Ina tsammanin wannan yana daga cikin dalilin da ya sa masarautar Oto Awori da amincewar majalisar sarakunan Jihar Legas, suka nada ni a kan wannan sarauta domin ci gaba da ayyukan hada kawunan jama’a da ci gabansu”.
 Dangane da irin halin da Najeriya take ciki, musamman tabarbarewar tsaro, sai Sarkin Kasuwar Alabar Rago, Alhaji Umaru ya ce, “Lokaci ya yi da dukkanmu, musulmi da kirista, za mu koma ga yawaita rokon Allah Ya kawo zama lafiya a kasar nan, Ya yi mana maganin wannan hali da muke ciki. Alheri ba ya sauka ga kasar dake cikin tashe-tashen hankula”.